Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Tsaurara Tsoro Yayin Da Ake Shirin Rantsar Da Sabon Shugaban Ƙasa

Jami’an tsaro sun tsaurara matakai a dandalin Eagle Square, wurin da ake bikin rantsar da sabon zababben shugaban ƙasa, Asiwaju ...


Jami’an tsaro sun tsaurara matakai a dandalin Eagle Square, wurin da ake bikin rantsar da sabon zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima don tabbatar da bikin ya wakana lami lafiya.

Titunan da ke zuwa dandalin Eagle Square sun kasance da shinge, kuma mutanen da ke da takardar shaida ta musamman ne kawai ake ba su damar shiga.

A yau Litinin, 29 ga watan Mayu Muhammadu Buhari yake mika mulki ga Bola Ahmad Tinubu a matsayin sabon shugaban kasar Najeriya.

Bola Ahmed Tinubu ya ci zaɓenshugaban ƙasar ne wanda aka yi ranar 25 ga watan Fabarairu na wannan shekara a ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar, sai dai ƴan hamayya na ƙalubalantar sakamakon a kotu.

No comments