Daga Muhammad Farouk An nada Farfesa Imam Yahuza Suleiman na Sashen Larabci na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya a matsayin babban magatak...
Daga Muhammad Farouk
An nada Farfesa Imam Yahuza Suleiman na Sashen Larabci na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya a matsayin babban magatakarda kuma Babban Jami’in Hukumar Kula da jarabawar Larabci da Nazarin Addinin Musulunci wato (NBAIS).
Wannan yana kunshe ne a cikin wata wasika mai kwanan wata 23 ga Mayu 2023 mai lamba HME/FME/ Vol.01/136/A; “Nadin na tsawon shekaru biyar ne (5)”, aka bayanna a wasikar.
Wasikar dai na dauke da sa hannun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Har ya zuwa lokacin da aka nada Farfesa Imam Yahuza Suleiman, malami ne a Cibiyar Ilimi ta Sashen Larabci ta Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.
Ya taba zama mataimakin magatakardar hukumar.
No comments