Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bayan Kwashe Awa 10 A Hannunsu, EFCC Ta Saki Tsohon Gwamnan Binuwe

  Daga Muhammad A. Dalhatu An saki tsohon gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwe daga hannun hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa z...

 


Daga Muhammad A. Dalhatu

An saki tsohon gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwe daga hannun hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC.

Daily Trust ta ruwaito yadda tsohon gwamnan ya amsa gayyatar hukumar da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Talata.

Ya isa ofishin shiyya na Makurdi na hukumar, wanda ke kan titin Alor Gordon a babban birnin jihar, tare da rakiyar wasu tsoffin masu taimaka masa guda biyu.

Mai taimakawa tsohon gwamnan kan harkokin yada labarai, Terver Akase, da kuma babban mataimakin na musamman kan ayyuka na musamman, Abraham Kwanhgu, an gansu tare da shi.

Masu bincike sun yi wa Ortom tuhume-tuhume kan kudaden da aka kashe a Binuwe a lokacin da yake gwamna.

Ortom ya bar bashin Naira biliyan 187.7 ga gwamnatin Reverend Father Hyacinth Alia.

A wani takaitaccen biki da aka gudanar a tsohon dakin liyafa na gidan gwamnati da ke Makurdi, Ortom ya shaida wa Alia cewa takardar mika mulki cikin kundi uku takaitaccen tarihin mulkinsa ne na shekaru takwas.

Gwamnan ya bayyana cewa jimillar kudaden shigar jihar a tsawon shekaru takwas da ya yi ya kai Naira biliyan 734.9 a watan Afrilun 2023 yayin da jimillar basussukan da jihar ta ciwo a cikin wannan lokaci ya kai Naira biliyan 187.7 wanda ya hada da na albashin da ba a biya ba, basussukan fensho, lamuni da sauransu.

Ya kuma sanar da magajinsa game da shirin musanya/rage bashi tsakanin jihar da gwamnatin tarayya zuwa naira biliyan 97.716.

Ortom ya bayyana cewa, kudaden da ake sa ran shigowarsu Naira biliyan 48, bayan rangwame kuma, za a samu ragin basussukan da aka tattauna zuwa N45.2billion, ta yadda za a yi kasa da jimillar bashin jihar.

Ya kuma bayyana cewa tuni gwamnatinsa ta samu amincewar rancen N41billion da kuma wani daga Babban Bankin Nijeriya na CBN, inda ya bukaci gwamnatin Alia da ta matsa lamba kan a saki kudin bayan rantsar da shi.


No comments