Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ina Da Kudurori Da Tsare-tsare Da Za Su Ciyar Da Kasuwarmu Gaba -Inji Zababben Shugaban Kasuwar Central Market Katsina

Kwamitin da ya gudanar da zaben shugabannin babbar kasuwar Katsina wato Fatima Baika Market ya bayyana Alhaji Shehu Kuza a matsa...


Kwamitin da ya gudanar da zaben shugabannin babbar kasuwar Katsina wato Fatima Baika Market ya bayyana Alhaji Shehu Kuza a matsayin sabon shugaban kasuwar. 

Shehu Kuza ya samu nasarar ne bayan da ya doke abokan takarar sa da kuri'u 439 yayin da mai bi mashi Rufa'i Ayis ya samu kuru'a 246 sai na uku Bishir Bodala ya samu kuru'a 266 na hudu Aliyu Alti yasamu kuru'a 83 sai na biyar Dr Sharif ya samu kuru'a 12.

Da yake bayyana sakamakon zaben, shugaban kwamitin gudanar da zaben Alhaji Sani Bello yace" a matsayi na na babban jami'in zaben  shugabannin wannan kasuwa ta central market, ina mai bayyana Alhaji Shehu Kuza a matsayin sabon shugaban wannan kasuwa sakamakon samun mafi rinjayen kuri'u a tsakanin yan takarar da suka nemi wannan matsayi", inji shi.

Da yake jawabi bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya samu nasarar zaben , sabon shugaban Alhaji Shehu Kuza ya bayyana kudurin sa na samar da tsare tsaren da zasu ciyar da kasuwar gaba. 

Ya nemi goyon bayan 'ya'yan kungiyar hadi da duk wadanda suka nemi matsayin da su taho a hada hannu tare domin bunkasa kasuwar  da inganta harkokin mambobin ta baki daya.

Sabon shugaban dai zai yi aiki ne tare sauran sabbin shugabannin kungiyar da aka zabe su lokaci guda a wajen zaben wanda ya gudana a ofishin kasuwar dake cikin babbar kasuwar ta birnin Katsina. 

Sauran shugabannin sun kunshi mataimakin shugaban da sakatare da ma'aji da mai binciken kudi da dai sauransu. 

No comments