Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sadik Ango Ba Zai Bada Kunya Ba, Inji Ali Baba

Daga Idris Umar, Zariya Dan majalisa Tarayya mai wakiltar mazabar Sabon Gari a sabuwar gwamnati, Honorabul Sadik Ango ya yi wali...


Daga Idris Umar, Zariya

Dan majalisa Tarayya mai wakiltar mazabar Sabon Gari a sabuwar gwamnati, Honorabul Sadik Ango ya yi walimar godiya ga Allah tare da jama'arsa karkashin jam'iyyarsa ta PDP a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.

Taron an gudanar da shi ne a gidan gonar mahaifin Dan majalisar wato Farfesa Ango Abdullahi tsohon shugaban jami'ar Ahmadu Bello Zariya da take kusa da barikin sojoji na Basawa.

Wakilinmu na cikin wakilan kafafen yada labarai da suka shaida yadda taron ya gudana.

Bayan an karbi baki daga bangarori da dama an yi kide-kide an ci abinci an farantawa juna rai sai aka gudanar da wasanin kwaikwayo daga 'yan wasan kwaikwayo daga jihohi daban-daban.

Bayan haka wakilinmu ya zanta da daya daga cikin jagororin tafiyar ta Sadik Ango Abdullahi a matsayin wakili a majalisar taraya wato Honorabul Ali Baba. 

Honorabul Ali Baba shi ne tsohon Dan majilisar jihar kaduna mai wakiltar Sabon Gari a wancan gwamnatin da ta wuce.

Honorabul Ali Baba ya ya bayyanawa manema labarai cewa da ikon Allah Honorabul Sadik Ango Abdullahi ba zai ba jama'ar karamar hukumar Sabon Gari kunya ba indai suna tare da shi.

Honorabul Ali Baba ya kara da cewa a saninsa da Sadik Ango matashi ne mai kishin kasa mai kishin matasa mai son ci gaban al'ummar kasa baki daya.

A son hak ne Ali Baba ya ce sanin waye Sadik Ango shiyasa ya tsaya ya bayar da lokacinsa don ganin ya sami nasara tun daga farko har karshe.

Bayan haka Ali Baba ya yi kira ga jama'ar karamar hukumar Sabon Gari da su bashi goyon baya don kawo ci gaban rayuwa.

Kuma ya yi fatan duk wanda suka taimaka wajen cin nasarar Sadik Ango Allah ya saka masu da Alherinsa. 

Ya kuma bai wa 'ya'yan jam'iyyar PDP su hada kansu waje guda domin samun nasara a kowacce gaba.

No comments