Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ba Zan Yi Bacci Ba Har Sai Na Tabbatar Da Cewa Da Ikon Allah Mun Shawo Kan Matsalar Tsaro –Gwamnan Zamfara

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal   Zan biya albashi kafin babbar sallah Zan tattauna da NECO da WAEC domin dalibanmu su rubuta jarabawa Kashe-ka...

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal
 
  • Zan biya albashi kafin babbar sallah
  • Zan tattauna da NECO da WAEC domin dalibanmu su rubuta jarabawa
  • Kashe-kashe a Zamfara abu ne mara dadi
  • Naira miliyan uku gwamnatin da ta gabata ta bari a asusun gwamnatin jihar Zamfara

Wannan ita ce cikakkiyar hirar da BBC Hausa ta yi da gwamnan Zamfara, Dauda Lawal dangane da lamuran dake faruwa a jihar da tirka-tirka siyasa da maida martani tsakanin gwamnatinsa da tsohuwar gwamnatin da ta gabata wacce ake zargi da tsiyata jihar baki daya kafin mika ragamar mulki ga sabuwar gwamnati. Jaridar MADOGARA ta rubuta muku cikakkiyar hirar domin amfanar masu karatunmu:

BBC HAUSA: gas hi yanzu ku san kwanaki goma sha bakwai, ana tunkarar sati uku da Allah ya ba ka kujerar gwamnan Zamfara, ya ka samu kanka a matsayin gwamna?

DAUDA LAWAL: Alhamdulillah! Mun amshi wannan mulki kuma kamar yadda nake zato abubuwan da na samu sun ma fi tunani na. Tunda muka amshi mulkin nan, mun samu asusun Zamfara babu kudi. Kusan asusu daya na gani wanda watakila na ce akwai miliyan uku ko na ce hudu….

BBC HAUSA: na naira ko na dala?

DAUDA LAWAL: na naira! Sannan yau jiharnan wata uku ba a biya albashi ba kuma har yanzu a kai ake. Sannan yau idan ka duba duk wata ma’aikata dake cikin jihar Zamfara, an yanke musu wuta. Ana bin su bashi, bashi na miliyoyi dari-dari. Yau idan ka duba, duk wata ma’aikata tun daga ta shari’a ko jami’an tsaro, yau ba a biya su kudaden da ake ba su na yau da kullum na tafiyar da harkokinsu ba fiye da wata uku.

Da na yi zama da Alkalai sun gaya min cewa wata uku ko kobo ba a ba su ba saboda haka yanzu ma ba a iya zama a yi shari’a don ko takardar da za su yi rubutu yanzu ba su da ita. Jami’an tsaro na zauna da su, yau wata uku ‘yan kudaden da ake ba su na yau da kullum da za su shiga can su fita can, yau babu su. Kai motocin ma da suke amfani da shi yanzu, wallahi ba su da tayoyi ballantana a ce maka kudin mai da makamantansu.

Yau ‘yan makaranta jiya an yi min waya a Cyprus cewa an kore su (daliban Zamfara), a Indiya an yi min waya an kore su. Yau da muke maganarnan, duk wani dalibi na jihar Zamfara (makarantun gwamnati) bai rubuta NECO ba, bai rubuta WAEC ba. Saboda ana bin gwamnati fiye da Biliyan daya da dari shida.

Yau idan ka je gidanmu na Kaduna na gwamnati, kotu ta kulle shi, ana bin mu kudi. Jiya-jiyan nan a nan Abuja, gidajenmu na gwamnati, kotu ta zo ta sa a kulle su.

BBC HAUSA: kafin ka samu wannan nasara ta zama gwamna, ka yi tunanin wadannan matsalolin?

DAUDA LAWAL: na yi tunanin wadansu daga cikinsu kamar yadda na ce, to amma abin da na zo na tarar sai na ga abin ma ya wuce ma misali.

BBC HAUSA: ka yi maganar kudi ka ce an bar wajen miliyan uku ka ce zuwa hudu na naira…

DAUDA LAWAL: ..kwarai da gaske!

BBC HAUSA: ….amma gwamnatin APC da ta tafi ta fito tana cewa ta bar kudi kusan biliyan ashirin (20) a asusun gwamnatin Zamfara harda wasu daloli kusan miliyan uku haka.

DAUDA LAWAL: na ji wannan, sannan na ce don Allah don Annabi, ina so a zo a nuna mana shin a wani asusu ne aka ajiye wannan kudi? Kuma sun san cewa suna da wannan kudin ashe keta ce ya hana cewa a biya ma’aikata kudadensu? Keta ce ya hana a bada kudaden da za a sayo sinadarai da za a kai ma’aikatar ruwa? Keta ce ya hana a biya ma ‘yan makaranta kudadensu? Keta ne ya hana a biya jami’an tsaro kudadensu? Keta ne ya hana duk wadannan kotu da muke fama da su da makamantansu ya hana a biya su? Don Allah ina roko a nuna min wani asusu ne kuma a nuna mana duniya shaidar cewa ga biliyan ashirin (20) da gwamnati ta bari.

BBC HAUSA: yanzu me ka fara da shi?

DAUDA LAWAL: na farko maganar ruwa. Ku san wata hudu babu ruwa a cikin garin Gusau. To alhamdulillahi a wannan sati na zagaya na je gidan ruwa na ga irin matsalolin da suke fama da shi. Na farko dai ba su da wuta, saboda an yanke wutarsu fiye da wata hudu. Na biyu; babu sinadaran nan da ake sanyawa wanda da shi ne za a iya tura ruwa al’umma su yi amfani da shi. Sai da na je na ciyo bashi aka sayo wadannan sinadarai. Kuma sannan da ikon Allah na samu wasu bayin Allah Indiyoyi da suka zo da wadansu ‘machine-machine’, wanda na roke su suka ba mu kyauta. ‘Machine’ din nan yanzu idan za a saye su za a kashe miliyan dari biyu.

BBC HAUSA: ka yi maganar yanzu ba kudi, ga shi har ka ciyo ba shi ka fara tunkarar matsalar ruwa. Ma’aikatan nan na Zamfara kusan watansu uku ko hudu ba albashi, kana ganin baida muhimmanci a samu su rage zafi musamman a wannan lokacin na janye tallafin mai?

DAUDA LAWAL: abin da zan iya tabbatar ma ma’aikatan jihar Zamfara da ikon Allah za mu yi kokari mu biya albashinsu kafin sallah. Duk yadda zan bi, hanyar da zan bi na biya albashi, idan Allah ya yarda, zan biya su.

BBC HAUSA: na wata nawa?

DAUDA LAWAL: toh, na farko zan ga bashin nawa ne za a iya ba ni. Idan zan iya biya fiye da wata daya, zan biya. Idan kuma ba zan iya ba, zan biya wanda na san cewa hakkina ne a wannan wata na ba su kafin na ga wacce hanya ce zan bi na samo wadansu kudaden don na tabbatar da cewa wannan bashi da suke bin gwamnati na dauke shi daga kan gwamnati.

BBC HAUSA: yanzu bari mu je kan tsaro; bayan hawanka kusan yanzu ka shaida irin kalubalen dake gabanka musamman an kai hare-hare a Maradun, an kai a yankin Maru, an kai kuma Jangebe har an kashe wani Likita…

DAUDA LAWAL: ….. a Makura ma an yi.

BBC HAUSA: a Makura ma an yi….

DAUDA LAWAL: kwarai da gaske.

BBC HAUSA: ya ka ji? Kuma me za ka yi?

DAUDA LAWAL: abu ne mara dadi, duk wani shugaba ba wanda zai so ya ji cewa yau an kashe wani mutumin jiharshi. Na ji zafin wannan abin, kuma na jajantawa wadannan al’umma. Muna nan muna bakin kokarinmu na tabbacin cewa an kawo tsaro a jihar Zamfara. Na farko cikin satin nan da ni da sauran gwamnonin Arewa ta yamma, mun zauna da shugaban kasa kuma mun gaya mishi irin matsalolin da muke fuskanta wajen tsaro, wanda ya tabbatar mana da cewa yana sane da wadannan matsaloli, kuma shima yana bakin kokari ya ga cewa an shawo kan wannan matsalar.

Bayan mun kammala wannan zama, na je na zauna da shi shugaban sojojin Nijeriya baki daya, wato shugaban Hafsan Hafsoshin tsaron Nijeriya ke nan, an sake tabbatar mishi da irin matsalolin da muke fuskanta na rashin tsaro. Ya ba ni tabbacin cewa a shirye suke su taimaka wajen kawo tsaro a Zamfara.

BBC HAUSA: to batun hanyoyin nan da ka yi magana a kai cewa kun tattauna wasu hanyoyi, akwai batun sulhu ciki?

DAUDA LAWAL: wato abubuwan suna da yawa. Abu ne da za a tattauna a gani, a ga cewa shin maganar sulhu ta ya za a bi idan ma sulhun za a yi. Ba zan iya gaya ma sauran abubuwan ba saboda abu ne na maganar tsaro, amma dai idan mun cimma iyaka, na san su da kansu jami’an tsaron za su fito su yi ma al’umma bayani kan irin matakan da aka dauka.

BBC HAUSA: wani alkawari za ka yi wa ‘yan Zamfara kan tsaron nan? Kila cikin kwanakinka 100?

DAUDA LAWAL: cikin abin da zan iya fada shi ne cewa maganar tsaro, ita ce kan gaba a kan wannan mulkina. Saboda haka ba zan yi bacci ba, ba kuma zan daga kafa ba, sai na tabbatar da cewa da ikon Allah mun ciwo kan matsalar tsaro a wannan jihar namu.

BBC HAUSA: to mu je batun ilimi, ka ce yara ba su rubuta jarabawa ba ga shi kuma an gaya maka cewa a Cyprus an kori daliban Zamfara, to yanzu batun ilimin nan kusan Zamfara ita ce baya, me ka shirya yi a gaggauce wanda kila zai iya tunkarar wannan matsalar?

DAUDA LAWAL: na farko abin gaggawa shi ne zan zauna da ‘yan NECO, da ‘yan WAEC domin mu shiga cikin wata yarjejeniya yadda zai iya biyan wadannan kudade da suke bin gwamnati wanda idan mun biya dalibanmu za su iya komawa makaranta, idan lokacin jarabawa ya yi kuma, za su iya zauna wa wannan jarabawa yadda za su amshi satifiket dinsu.

No comments