Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Kano Ya Maida Barista Muhyi Rimin Gado Kan Muƙaminsa Da Ganduje Ya Cire Shi

Daga Husaini Ahmad  Alhaji Abba Kabir Yusuf, Gwamnan jihar Kano, ya amince da mayar da Barista Muhyi Magaji Rimin Gado a matsayi...

Daga Husaini Ahmad 

Alhaji Abba Kabir Yusuf, Gwamnan jihar Kano, ya amince da mayar da Barista Muhyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar karbar korafe-korafen Jama’a da yaki da cin hanci da rashawa wato PCACC domin kammala wa’adinsa.

Wannan bayanin ya fito ne a sanarwar da Sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Laraba 21 ga watan Yunin 2023. 

Idan za ku iya tunawa gwamnatin da ta gabata ne ta dakatar da Barista Muhyi daga mukaminsa bisa wasu dalilai.

Maido da aikinsa zai soma aiki nan take kuma yana da alaka da bin umarnin kotu. 

No comments