Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Ta Karawa Shugaban Kasa, Mataimakinsa, Gwamnoni Da Sauran Zababbu Albashi

Daga Muhammad Farouk Gwamnatin Tarayya ta amince da karin albashi da kashi 114% ga shugaban kasa, mataimakinsa da kuma zababben gwamnoni. Hu...

Daga Muhammad Farouk

Gwamnatin Tarayya ta amince da karin albashi da kashi 114% ga shugaban kasa, mataimakinsa da kuma zababben gwamnoni.

Hukumar tattara kudaden shiga da raba su da kuma kasafin kudi (RMAFC) ta amince da karin kashi 114 na albashin zababbun ‘yan siyasa da suka hada da shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, gwamnoni, ‘yan majalisa da ma’aikatan shari’a da na gwamnati.

RMAFC ce take da alhakin tantance albashin da ya dace ga masu rike da mukaman siyasa da suka hada da Shugaban kasa, Mataimakin Shugaban Kasa, Gwamnoni, Mataimakan Gwamnoni, Ministoci, Kwamishinoni, Masu Ba da Shawara na Musamman, ‘Yan Majalisa da masu rike da ofisoshi kamar yadda aka ambata a sashe na 84 da 124 na Kundin Tsarin Mulki. 

Hukumar ta bukaci majalisun dokokin jihohi 36 da su gaggauta yin gyare-gyare kan dokokin da suka dace domin ba da damar sake duba kunshin albashin ma’aikatan siyasa, shari’a da na gwamnati.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya wato NAN ta ruwaito, Shugaban RMAFC, Muhammadu Shehu wanda Kwamishiniyar Tarayya Rakiya Tanko-Ayuba ta wakilta ta yi wannan kiran ne a wajen gabatar da rahoton kunshin albashin da aka yi wa kwaskwarima ga gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, ranar Talata a Birnin Kebbi.

Ya ce aiwatar da tsarin biyan albashin da aka yi wa gyara ya fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Junairu, 2023, inda ya ce an dauki matakin ne bisa tanadin sakin layi na 32(d) na sashi na 1 na jadawali na uku na kundin tsarin mulkin gwamnatin tarayya na shekarar 1999 (kamar yadda aka gyara).

Ya ce an gudanar da bitar albashin na karshe ne a shekarar 2007, inda ya bayyana cewa ya tsaya ne a “wasu daga cikin masu rike da mukaman siyasa da na gwamnati da na shari’a (albashi da alawus-alawus da sauransu) (a kudurin gyararren doka na) 2008”.

No comments