Bayan koran dukkan Hafsan Hafsoshin tsaron Nijeriya baki daya, Manjo Janar Christopher Gwabin Musa memba a Course 38 Regular Course na ta ...
Bayan koran dukkan Hafsan Hafsoshin tsaron Nijeriya baki daya, Manjo Janar Christopher Gwabin Musa memba a Course 38 Regular Course na ta makarantar sojoji ta NDA ya zama sabon shugaban Hafsan Hafsoshin tsaron Nijeriya inda zai karbi ragamar mulki daga hannun Janar Lucky Irabor.
An haifi Manjo Janar C.G Musa a jihar Sakkwato ta Arewa maso Yamma a ranar 25 ga Disamba, 1967.
Musa ya yi firamare da sakandire a Sakkwato, duk da cewa ya fito daga karamar hukumar Zangon Kataf ta Kudancin Kaduna.
An shigar da babban hafsan sojan ne a NDA a shekarar 1986 inda ya yi horon soji na tsawon shekaru biyar a lokacin da sojoji ke rike da madafun iko a kasar.
A cikin watan Satumban 1991, aka ba shi aikin sojan Nijeriya a matsayin laftana na biyu a rundunar sojojin kasa a bangaren 'Infantry' a daya daga cikin sassan da suka fi wahala a bangaren sojojin.
Har ya zuwa sabon nadin nasa, a shekarar 2021, aka sake tura shi ya zama kwamandan rundunar hadin gwiwa (a Arewa maso Gabas), kuma Atisayen Lafiya Dole wanda daga baya ya zama atisayen Hadin Kai.
No comments