Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ko Kun San Wane Ne Shugaban Riko Na Hukumar EFCC?

  Daga Muhammad A. Dalhatu Bayan dakatar da Abdulrasheed Bawa a ranar Talata, a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki...

 

Daga Muhammad A. Dalhatu

Bayan dakatar da Abdulrasheed Bawa a ranar Talata, a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) da shugaba Bola Tinubu ya yi, Abdulkarim Chukkol ya zama sabon shugaban riko na hukumar.

Har zuwa sabon mukaminsa, Mista Chukkol shi ne daraktan ayyuka na hukumar.

Babban ma’aikacin hukumar kuma fitaccen memba na EFCC na 'Cadet Course One', Mista Chukkol kwararren mai bincike ne da ya kware a harkar binciken laifukan yanar gizo da halasta haramtattun kudade.

Mukaminsa a hukumar ya hada da Kwamandan yaki da damfara da laifukan yanar gizo na shiyyar Legas da Abuja tsakanin 2011-2016, kwamandan shiyyar Uyo a 2017 da kwamandan shiyyar Fatakwal a 2020.

Mista Chukkol ya halarci ayyuka na musamman da dama tare da kungiyoyin tilasta bin doka da oda na kasa da kasa kuma yana da kusanci da hukumomin tilasta bin doka kamar su FBI, Hukumar yaki da Laifuka na Kasa ta Birtaniya, Hukumar Binciken takardun Amurka (USPIS), Hukumar jami'an sirri ta Amurka, 'Yan sandan Ostireliya, 'yan sandan Dutch, 'yan sandan Jamus, 'yan sandan Afirka ta Kudu, da dai sauransu.

Mukaddashin shugaban na EFCC ya yi aiki kafada da kafada da sauran gwamnatoci domin bunkasa doka da kayayyakin gudanar da ayyuka domin aiwatar da su wajen tabbatar da doka da oda.

Shi ne jami'in tuntuba na Nijeriya a kungiyar 'International Mass Marketing Fraud Working Group' mai wakiltar manyan hukumomin gwamnati, jami'an tsaro, masu gabatar da kara, shige da fice da kwastam, bayanan kudi, hukumomin kare masu huldar kasuwanci da gasa da ke kula da al'amurran da suka shafi huldar kasuwanci mai yawa daga kasashen Sipaniya, Nijeriya, Belgium, Europol, Canada, United Kingdom da kuma Amurka.

Ya halarci kwasa-kwasai da yawa, tarukan karawa juna sani da kuma tarukan horaswa kan cin hanci da rashawa, zamba da sauran laifukan tattalin arziki da na kudi a cikin gida da waje, ciki har da Jami'ar Oxford, United Kingdom, a shekarar 2022.

Ayyukansa da tunaninsa a tsawon shekaru ya janyo masa samun lambar yabo da jinjina da dama a cikin gida da waje, ciki har da "Kyauta ta mafi kyawun aiki" da EFCC ta ba shi da kuma "mafi kwarewa" ta ma'aikatar shari'a ta Amurka, da sauransu.

Mukaddashin shugaban hukumar na EFCC, ya yi digirinsa na farko a fannin tattalin arzikin gona daga jami’ar Maiduguri (2000) da kuma takardar shaidar kammala karatun digiri na biyu a fannin shari’a a jami’ar Virginia, ta kasar Amurka, haka kuma ya yi digirin digirgir a fannin tsaro ta yanar gizo da sarrafa 'spectrum'.

Sannan tsohon dalibi ne a Cibiyar Nazarin Kasa ta FBI, Quantico; Cibiyar Nazarin Tsaro ta Turai, Jamus, kuma dalibi ne a Kwalejin Yaki, Nijeriya.

No comments