Daga Ammar Muhammad Rajab Wata babbar kotu a Kaduna ta yi watsi da karar da tsohon gwamnan jihar, Nasir el-Rufai ya shigar kan tsohon San...
Daga Ammar Muhammad Rajab
Wata babbar kotu a Kaduna ta yi watsi da karar da tsohon gwamnan jihar, Nasir el-Rufai ya shigar kan tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani.
El-Rufai dai ya nemi a biya shi diyyar Naira biliyan 2 a kan kalaman da ya ce Shehu Sani ya yi akansa na bata masa suna.
A karar da ya shigar a shekarar 2018, tsohon gwamnan ya ce Sani ya bata masa suna ne ta hanyar kiransa da cewa “mai shaye-shaye, kuma abin kunya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari”.
El-Rufai ya yi ikirarin cewa kalaman Sani kwata-kwata karya ce da cutar da shi a idon jama’a.
Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Alkalin kotun, H.A.L Balogun, ya ce karar cin zarafin kotu ne.
Balogun ya ce El-Rufai ne ya shigar da karar a kotuna daban-daban a jihar.
A lokacin da aka fara sauraren karar, lauyan Sani, Kimi Livingstone Appah, ya ja hankalin kotun kan yadda tsohon gwamnan ya shigar da karar a wasu kotuna hudu da ke jihar.
Alkalin ya yadda da binciken Appah kuma ya yi watsi da karar.
Da yake ganawa da manema labarai bayan hukuncin kotun, Appah ya ce; "wannan nasara ce ga dimokuradiyya da kuma 'yancin fadar albarkacin baki".
Dama El-Rufai da Shehu Sani ba a jituwa kan batutuwa da dama da suka shafi jihar Kaduna.
No comments