Daga Ammar Muhammad Rajab An nada Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, mai...
Daga Ammar Muhammad Rajab
An nada Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro, a yayin da Wale Edun ya zama mai ba da shawara na musamman kan harkokin kudi ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu.
An sanar da nadin nasu ne a ranar Alhamis a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Abiodun Oladunjoye, Daraktan yada labarai na fadar gwamnatin Tarayya.
Baki daya, shugaban ya nada mutane takwas a matsayin masu ba shi shawara na musamman.
An nada Yau Darazo mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa da na gwamnatoci, a yayin da aka nada Olu Verheijen mai ba da shawara na musamman kan makamashi.
Shugaban kasar ya kuma nada Zachaeus Adedeji a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin kudaden shiga, a yayin da John Ugochukwu Uwajumogu aka nada shi mai ba shi shawara na musamman kan harkokin masana’antu, kasuwanci da zuba jari.
An nada Salma Ibrahim Anas mai ba shi shawara na musamman kan harkokin lafiya.
Shugaban ya ce nade-naden sun fara aiki nan take.
A ranar 6 ga watan Yuni, 2023, majalisar Dattijai ta amince da bukatar Tinubu na nada masu ba shi shawara na musamman guda 20.
No comments