Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YANZU-YANZU: Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC Saboda Wuce Makaɗi Da Rawa

Daga Zailani Mustapha Labarin dake shigowa Jaridar MADOGARA na nuni da cewa; shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da shugaban hukumar...


Daga Zailani Mustapha

Labarin dake shigowa Jaridar MADOGARA na nuni da cewa; shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Abdurrasheed Bawa bisa amfani da ofishinsa yana wuce makadi da rawa. 

Sanarwar dakatar da shi ta fito ne daga ofishin Sakataren gwamnati a sanarwar da ya fitar dauke da sa hannun, Daraktan yada labarai na ofishin, Willie Bassey.

Sanarwar ta ce an dakatar da Abdurrasheed Bawa domin ya koma gefe a binciki korafin da aka shigar a kansa. 

Sanarwar ta jaddada cewa gwamanti ta dauki wannan matakin ne biyo bayan "manya-manyan zarge-zarge" da aka yi wa Abdurrasheed Bawa. 

“Ana umurtar Bawa da ya mika ragamar shugabancin hukumar ga Babban Darakta a hukumar, wanda zai ci gaba da gudanar da hukumar har zuwa lokacin da za a kammala bincike", inji sanarwar. 


No comments