Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Siyasa Ta Ƙare, Yanzu Lokaci Ne Na Ceto Zamfara -Gwamna Lawal Ga Sabbin ‘Yan Majalisa

  Daga Muhammad A. Abubakar  Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya buƙaci sabbin ‘yan majalisar dokokin jihar Zamfara da su haɗa kai domin ...

 


Daga Muhammad A. Abubakar 


Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya buƙaci sabbin ‘yan majalisar dokokin jihar Zamfara da su haɗa kai domin yi wa jihar aiki.


Lawal ya yi wannan roƙon ne a ranar Talata a lokacin da yake ganawa da sabbin ‘yan majalisar da aka ƙaddamar a zauren majalisar dake fadar gwamnatin jihar Zamfara.


A jiya ne majalisar dokokin jihar Zamfara ta ƙaddamar da membobinta a majalisar ta 7 tare da zaɓar shugabanninta kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada.


An zaɓi Hon. Bilyaminu Ibrahim Moriki (Zurmi ta Arewa) a matsayin shugaban majalisar wakilai ta bakwai ba tare da hamayya ba.


A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce Lawal ya karɓi jagorancin majalisar ta bakwai ne domin sanin juna.


Ya buƙaci ‘yan majalisar da su ci gaba da ƙulla kyakkyawar alaƙa da ɓangaren zartarwa ta gwamnati.


Gwamna Lawal ya ce, “Ina so na yi amfani da wannan damar domin taya ‘yan majalisar 24 murnar ƙaddamar da su a yau. Aikin da ke kanku bisa kundin tsarin mulki wanda aka zaɓe ku dominsa aiki ne babba. Ina mai tabbatar muku da cewa gwamnatina a shirye take ta haɗa hannu da majalisar dokokin ta jiha, kuma dole ne mu yi aiki tare domin ɗorewar ƙawancen.


“Zamfara na fuskantar manyan ƙalubale da suka haɗa da rashin tsaro zuwa ga taɓarɓarewar ilimi, da dai sauran muhimman batutuwan da yakamata a maida hankali a kai.


“Siyasa ta ƙare, lokaci ya yi da za a haɗa kai domin musayar fahimtoti domin ɗaga darajar jihar Zamfara.”


Tun da farko, Kakakin majalisar, Hon. Bilyaminu Ibrahim Moriki ya ce ‘yan majalisar za su bayar da cikakken goyon baya tare da haɗin kai ga ɓangaren zartarwa domin ci gaban jihar.

No comments