Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Al'umma na Allah-wadai da rushe shatale-telen gidan gwamnatin Kano da Abba Gida-Gida ta yi

Daga Muhammad Farouk Da safiyar yau Laraba 14 ga watan Yunin 2023 aka wayi gari da gwamnatin NNPP ta Abba Kabir Yusuf ta rushe S...


Daga Muhammad Farouk

Da safiyar yau Laraba 14 ga watan Yunin 2023 aka wayi gari da gwamnatin NNPP ta Abba Kabir Yusuf ta rushe Shatale-telen dake gaban gidan gwamnatin jihar Kano. Lamarin da ya fusata al'umma a shafukan sada zumunta da kuma garin Kano.

Da dama da muka zanta da su sun nuna damuwarsu da rashin gamsuwarsa bisa rushe wurin. Sun kuma nema gwamnatin jihar ta fito ta yi gamsasshen bayani kan lamarin. 

Wasu na ganin rushe-rushen da sabuwar gwamnatin jihar Kano take gudanarwa wanda Abba Kabir Yusuf yake ma jagoranci, wadda ta kai ga ugurguza shatale-talen dake gaban gidan Gwamnatin jihar ta Kano, wanda shi ne É—aya daga cikin wurare mafi kyau a fadin jihar ta Kano ba tare da wani dalili ko hujja gamsasshe ba ko umurnin kotu ya zuwa haÉ—a wannan rahoto kamar bita da kulli ne ga gwamnatin da ta gabace ta. 

Wasu masu sharhi masu ganin bita da ƙulli ne kawai sabuwar gwamnati ke yi wa gwamnatin da ta gabata har a abubuwan da ya shafi al'umma kai tsaye suna ganin babu dalilin rushe wannan muhalli. Da dama sun tofa albarkacinsu a shafukan sada zumunta musamman Facebook, inda suke Allah-wadai bisa rushe wannan shatale-tele da ya shiga kundin tarihi kuma ya zama alamin al'ummar Kano.

Rusau É—in bayanai ya nuna cewa dai ya gudana ne a cikin daren jiya Talata. 

Zuwa yanzu dai an rushe kadarorin biliyoyi daga karbar gwamnatin Abban. 

No comments