Daga Hussaini Ibrahim Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta zabi Kakakinta karo na bakwai daga mazabar Moriki daga Karamar hukumar ...
Daga Hussaini Ibrahim
Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta zabi Kakakinta karo na bakwai daga mazabar Moriki daga Karamar hukumar Zurmi ta Arewa. Sai kuma mataimakinsa Hon. Adamu Aliyu daga mazabar Gumi ta biyu.
Akawun Majalisar dokokin jihar Zamfara, Shehu Sai'du Anka ya jagoranci zaben shugabannin majalisar.
Kuma nan take Akawun majalisar dokokin ya rantsar da Kakakin Majalisar kamar yadda doka ta tanada.
Haka kazalika ma Kakakin majalisar dokokin Jihar Zamfara, Hon. Bilyaminu Isma'il ya rantsar da sauran shugabannin Kwamitocin zauren majalisar domin fara aikinta a yau Talatar nan.
No comments