Masarautar Zazzau ta soke bikin hawan daba a bikin Babbar Salla mai zuwa. Jaridar Daily Trust ta ruwaito Mallam Yusuf Abubakar H...
Masarautar Zazzau ta soke bikin hawan daba a bikin Babbar Salla mai zuwa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Mallam Yusuf Abubakar Hayat, sakataren masarautar yana sanar da wannan mataki a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 12 ga watan Yuni.
Ya ce matakin ya zo ne bayan tafiyar da Mai martaba Sarkin Zazzau Mallam Ahmed Nuhu Bamalli ya yi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.
Sanarwar ta kara da cewa, Sarkin wanda tuni ya taya al'ummar masarautarsa ta Zazzau murnar barka da sallah, ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar Najeriya su gudanar da addu’o'i don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
Majiyarmu ta BBC Hausa ta ce ana shafe tsawon kwana uku ana hawan dawaki a Masarautar Zazzau duk shekara, a wani ɓangaren na bikin babbar salla.
No comments