Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matsalar Tsaro: Gwamnan Zamfara Ya Ziyarci Shugaban Hafsan Hafsoshin Tsaron Nijeriya

  Daga Muhammad A. Abubakar Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Juma'a, ya nemi karin tallafin sojoji domin shawo kan matsalolin...

 

Daga Muhammad A. Abubakar

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Juma'a, ya nemi karin tallafin sojoji domin shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar jihar.

Gwamna Lawal, ya nemi goyon bayan sojojin ne da kasancewarsu a ziyarar da ya kai wa babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya, Janar Lucky Irabor a hedikwatar tsaro da ke Abuja.

Sanarwar da Kakakin Gwamnan Jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa ziyarar na daya daga cikin kokarin da Gwamna Lawal ke yi na wanzar da zaman lafiya da tsaro a jihar Zamfara.

“Gwamna Lawal ya ziyarci hedikwatar tsaro ne na musamman domin ya yaba musu bisa kokarin da sojoji ke yi a yaki da ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

“Ya yi ganawar sirri da babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor, domin tattauna muhimman batutuwan tsaro da kuma hanyar da za a bi wajen magance su.

“Kudirin gwamnatinmu ne ta amince da alhakin da ya rataya a wuyan gwamnatin tarayya kan harkokin tsaron cikin gida, wanda ya hada da alaka ta kusa da sojoji.

“Gwamnan ya damu da rashin tsaro da ake fama da shi a wasu yankunan jihar Zamfara, domin haka ne yake aiki kafada da kafada da duk masu ruwa da tsaki a hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya.”



No comments