Gwamnan jihar Adamawa Ahamdu Umaru Fintiri ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan kisan wani matashi mai shekara 17 da ake zargin jami...
Gwamnan jihar Adamawa Ahamdu Umaru Fintiri ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan kisan wani matashi mai shekara 17 da ake zargin jami'an sinitiri na Operation Farauta da yi a Yola, babban birnin jihar.
Wata sanarwa da sakataren watsa labaru ga gwamnan, Humwashi Wonosikou ya fitar, ta ce gwamnan ya umarci kwamishinan ƴan sanda a jihar da ya fara bincike kan lamarin domin kama waɗanda suke da hannu.
Matashin mai suna Abdullahi Tukur Abba ya rasu ne a ranar Laraba da ta gabata a asibitin koyarwa na Jami'ar Modibbo Adama da ke Yola, bayan gallaza masa da ake zargin jami'an sinitirin da yi.
Tun da farko dai, rahotanni sun bayyana cewa an kama matashin a ranar 5 ga watan Agusta bayan da wani makwaɓci ya kai ƙarar cewa ya sace masa waya.
Sanarwar ta jajantawa ƴan uwan mamacin tare da kiran cewa su kwantar da hankali domin gwamnati za ta tabbatar da cewa an yi adalci a lamarin.
Lauyan iyalan mamacin ya ce bayan duka da jami'an na Operation Farauta suka yi wa Abdullahi, daga baya wani matashi ya fito tare da cewa shi ya sace wayar da ake zargin Abdullahi da yi.
Rundunar ta Operation Farauta ta kunshi haɗin gwiwar sojoji da ƴan sanda da jami'an farin kaya DSS da kuma ta kare fararen hula ta cibil defence.
No comments