Raphael Varane ya ci wa Manchester United kwallon da ta ba ta nasara a kan Wolves ana saura mintuna 14 a tashi daga wasan da suka gwabza...
Raphael Varane ya ci wa Manchester United kwallon da ta ba ta nasara a kan Wolves ana saura mintuna 14 a tashi daga wasan da suka gwabza a daren Litinin a gasar Firimiyar Ingila, wasan da aka yi amannar United ta tsallake rijiya da baya.
Tawagar ta Erik ten Hag ta samar da damammaki na cin kwallaye masu armashi amma babu nasarar sanya ko da guda a raga, sai bayan da Bruno Fernandes ya saka wa Aaron Wan-Bissaka wata kwallo shi kuma ya jefa ta cikin gidan Wolves,inda a nan ne Varane ya yi amfani da tsayinsa ya sa mata kai ta shiga raga.
Wannan lamari ya yi wa Wolves ciwo ainun, ganin cewa kocinta, Gary O’Neil yana neman nasararsa ta farko a wannan kungiya da ya karbi aikin horar da ita.
O'Neil ya samu katin gargadi a lokacin da ya yi ta hargowa yana neman alkalin wasa ya ba tawagarsa bugun daga kai sai mai tsaron raga a kusan karshen wasa.
A nasa bangaren, mai tsaron ragar United, wanda yake wasan Firimiya a karon farko ya tsallake rijiya da baya, saboda ya yi sa’a ba a sallame shi daga wasa ba duk da karon da ya yi da Sasa Kalajdzic ba tare da ya taba kwallo ba.
No comments