Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mutum 350 Ne Suka Amfana Da Tallafin Babura, Injin Markade Da Atamfofi Daga Dan Majalisar Tarayya A Katsina

Daga Awwal Jibril 'Yankara A ranar Asabar 19/8/2023 Dan Majalisar Tarayya Mai wakiltar kananan Hukumomin Kankara, Faskari da Sabuwa a ma...


Daga Awwal Jibril 'Yankara

A ranar Asabar 19/8/2023 Dan Majalisar Tarayya Mai wakiltar kananan Hukumomin Kankara, Faskari da Sabuwa a majilisar wakilai ta kasa dake Abuja wato Hon. Jamilu Mohammad Lion (Magayakin Faskari) ya raba  Babura da injin markade sama da guda 350 a garin Faskari dake karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina. 

Wakilinmu ya labarto mana cewa; dan Majalisar Tarayar ya yi kira ga al'ummar da suka amfana da wannan kayan da su yi amfani da shi ta hanyar da ta dace domin samun abin kudaden shiga.  

A lokacin da yake raba kayan sana'ar ga matasa da mata ya yi kira ga wanda ba su samu ba da su yi hakuri yanzu aka fara .

Dama a ranar rantsar da shi a watan Yulin 2023, Dan Majalisar Hon. Jamilu Muhammad (Dan Zaki) ya yi ma matasa alkawarin tallafa masu su dogara da kansu. 

Wannan shi ne karo na 3 da ya tallafawa al'ummar kananan Hukumomin Kankara, Faskari da Sabuwa. 

Wadanda suka amfana sun shaida ma wakililnmu cewa wannan babban abin a yaba ne kuma babban abin alfahari ne ga yankin baki daya. 

Shugaban Jam'iyar PDP na karamar Hukumar Sabuwa Hon. Aliyu Hassan ya yaba ma dan majalisar bisa irin wannan namijin kokari da ya yi na tallafa ma mutane a irin wannan lokaci da ake fama da kai.

Da yake amsa tambaya kan halin rashin tsaro da ke fuskantar kananan hukumomin da yake wakilta Hon. Jamilu Muhammad (Dan Zaki, Magayakin Faskari, Sarkin Matasan Abuja), ya ce ga duk mai bibiyarsa a wannan sha'ani ya san abin da ya fara da shi ke nan a majalisa kuma haka ya je ya sami Gwamna Dr. Dikko Radda a matsayin shi na babban shugaban tsaro na jiha kuma yai mai alkawarin hada hannu domin a shawo kan matsalar tsaron, in ji shi. 

No comments