Daga Auwal Jibrin ‘Yankara Aliyu Hassan, shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina ya jinjinawa Dan Majalisar Tara...
Daga Auwal Jibrin ‘Yankara
Aliyu Hassan, shugaban
jam’iyyar PDP na karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina ya jinjinawa Dan Majalisar Tarayyarsu mai
wakiltar kananan Hukumomin Kankara, Faskari da Sabuwa a majilisar wakilai ta
kasa dake Abuja wato Hon. Jamilu Mohammad Lion (Magayakin Faskari) bisa raba
Babura da injin markade sama da guda 350 a garin Faskari dake karamar hukumar
Faskari ta jihar Katsina.
Shugaban jam’iyyar ya
bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da wakilinmu a yayin raba wadannan
kayayyakin.
Hassan ya ce; “kowacce
karamar hukuma yanzu haka ya sa a je a katangewa ‘yan sanda ofishinsu. Kowacce
karamar hukuma ya sa an sanya jami’an tsaron ‘yan sandan Mopol guda
talatin-talatin domin a sake samar da tsaron a wadannan yankuna”, in ji shi.
Shugaban jam’iyyar PDP
na karamar hukumar ta Sabuwa ya ci gaba da cewa; “kuma yanzu ga Babura wanda ya
bai wa jam’iyya da matasa wadanda suka jajirce lokacin da ake neman wannan
tafiya. Ya ce tunda Allah ya kai shi bari ya kyautata musu”, ta lurantar.
Hassan ya ce idan aka
cire Maigidansa Sanata Lado Danmarke babu wanda ya taba kwatanta abin da dan
majalisar ya yi na kyautatawa al’ummar mazabarsa.
“Ita siyasa alkibla ce.
Fatanmu matakin da ya taka daga majalisar wakilai ya kai har zuwa matsayin
Gwamna”, ya yi addu’a.
Daga karshe ya yi kira
ga al’umma da cewa; ita wannan tafiyar ta kowa da kowa ce, bad an PDP bad an APC
bad an APGA; “abin da yake so kawai mai kishi kuma jajirtacce. Kuma muna ganin
yadda yake nuna kishinsa. Bisa haka ne ma ya nema wa al’umma aiki a bangaren
hukumar shige da fice, da sojoji. Bai yi la’akari da dan jam’iyya ba, cewa ya
yi a duba wanda ya cancanta ya wakilci al’ummarmu. Wanda idan aka tashi za a ce
mutumin kirki aka tura”, ya jaddada.
No comments