Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Karrama Shaikh Zakariyya Usman

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna Sakamakon aiki tukuru wajen karantar da dimbin al'umma ilimin addinin musulunci da kuma bunkasa tattalin a...



Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

Sakamakon aiki tukuru wajen karantar da dimbin al'umma ilimin addinin musulunci da kuma bunkasa tattalin arzikin arewacin Najeriya da kasa baki daya ya sa kungiyar yan jarida masu wallafa jaridu da mujallu ta Arewa mai suna "Arewa Publishers Forum" karkashin Dakta Sani Garba suka karrama Shaikh Zakariyya Usman da nufin sauran jama'a su yi koyi da ayyukan ci gaban al'umma da Shaikh Zakariyya Usman yake aiwatarwa.

Jim kadan bayan karrama shi a cikin jawabinsa da ya gudanar Shaikh Zakariyya Usman ya karantar da duniya kamar yadda ya saba da niyyar kowa zai samu babban rabo a duniya da lahira kamar haka.

Inda Shaikh ya ce "Babban abu mai muhimmanci shi ne mutum ya kara neman sanin Allah sannan ka bauta masa dogara gare shi sannan a  bauta masa kuma mutum ya zamanto duk abin da yake yi da gaske mutum yake yi domin Allah gaskiya ne, Manzon Allah gaskiya ne kuma addinin musulunci gaskiya ne, ranar tashin kiyama gaskiya ne sannan kuma ayi hakuri saboda sai da hakuri ake cin nasara.

Shaikh Zakariyya Usman ya kuma fadakar da al'umma cewa mutum ya zama ya na da ikilasi kasancewar ikilasi ne mai daukar ayyuka zuwa sama zuwa wajen madaukakin sarki Allah, ta hanyar tauhidi kuma kadaita Allah abu ne mai muhimmanci kwarai a rayuwar jama'a kasancewar Allah ne wanda ba a yin tarayya da sunayensa don haka sai dai a bauta masa shi kadai kada a hada shi da dukkan komai.

Shaikh kuma ya ci gaba da fadakar da al'umma a kan horon da rikon Amana kada mutum ya ci Amana, mama's kuma su kasance masu yarda da Kaddara, sannan Allah na son godiya, saboda haka ne shaidan ya ce ba zan bari bayinka su gode maka ba a Kan abin da ka yi masu ba sai Allah ya ce ba zaka samu iko a kan bayi na ba, ikilasi na da muhimmanci kwarai da gaske sannan istigfari kasancewar dukkan yan Adam masu kurakurai ne amma fiyayyen ku shi ne wanda ke yin istigfari don haka a rika neman tuba.

Shaikh ya kara da cewa ya dace mutane su rika yin goyi da Manzon Allah Annabi muhammadu SAW da ya kasance mai yi wa Allah godiya ta hanyar yin Istigfari domin wani hadisi ya ce ya na yin tuba sau saba'in sai kuma na uku a cikin rukunnan musulunci Zakka saboda haka ya dace a san cewa rukunnan musulunci biyar na da muhimmanci a koda yaushe. Aikin hajji da kuma Azumi kun ga a kwai lokacin da nisabin Zakka yake a naira dubu Bakwai (7000) saboda a can baya lokacin mulkin Buhari da Ediyabon na farko kudin Najeriya ya yi daraja kuma kudin Sadaki bai wuce naira daya ba,amma a yanzu kudin nisabin Zakka sai kudin ka ya kai naira miliyan biyu da dubu dari biyu (2.2) kuma idan mutum kudinsa bai kai nisabin Zakka ba to sai ayi sadaka kuma akwai lokutan Idi guda biyu na farko da idin babbar Sallah za a yi yanka a rabawa jama'a sadakar naman saboda haka muna yin addu'a ga Allah madaukakin sarki ya bamu ikon yi kuma in mun yi Allah ya karba mana abin da muke karantar da jama'a Allah ya albarkace su.

Shaikh Zakariyya ya kuma yi addu'a ga manema labarai da suke yi wa jama'a aiki da Allah ya saka masu da alkairi ya Sanya albarka a cikin ayyukan da suke yi. Ya kuma yi addu'a ga yaya da cewa dukkan karatun addinin musulunci da mu ba mu yi na Allah yasa yayan mu su yi shi Allah ya Sanya mu gama da duniya lafiya ya Sanya Aljannah ta zama makomar mu kuma dukkan abin da ya ke shafar musulmi da ba dadin ji Allah ya yaye mana shi gaba daya.

Ina yi wa yan jarida da kuka zo kuka same ni babbar godiya kwarai, ina yi wa Allah godiya a bisa hakan.

No comments