Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tallafin da gwamnmatin Legas za ta yi domin sassauta ƙuncin rayuwa

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana wasu jerin matakai da gwamnatinsa za ta ɗauka domin kawo sassauci ga al’ummar jihar sanad...



Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana wasu jerin matakai da gwamnatinsa za ta ɗauka domin kawo sassauci ga al’ummar jihar sanadiyyar matsin rayuwa da ake fuskanta a faɗin ƙasar.

Matsin rayuwar da al’ummar Najeriya ke ciki dai ya janyo zanga-zanga a wasu jihohin ƙasar, ciki har da Kano da Oyo da kuma Osun.

Ana ɗora alhakin tsadar rayuwar da mutane ke fuskanta ne a kan matakan da gwamnatin tarayyar ƙasar ta ɗauka na cire tallafin man fetur da kuma barin kasuwa ta tantance farashin dalar Amurka.

Lamarin ya haifar da tashin gwauron-zabi na farashin kayan abinci da na masarufi da kuma rashin albarkar kuɗin da ke hannun al’umma.

Sanadiyyar hakan ne gwamnan jihar Legas a ranar Alhamis ya gabatar da jawabi ga al’ummar jihar tare da sanar da ɗaukan wasu matakai, waɗanda ya ce za su taimaka wajen rage ƙuncin rayuwa da al’umma ke fuskanta.

Wasu daga cikin matakan su ne:

Rage ranakun aikin gwamnati zuwa uku a mako

Gwamnan Sanwo-Olu ya sanar da cewa ma’aikatan gwamnati daga mataki na 1 har zuwa na 14 za su fara zuwa aiki kwana uku a mako.

Ma’aikata daga mataki na 15 zuwa 17 kuma za su riƙa zuwa aiki sau huɗu a mako.

To sai dai matakin bai shafi malaman makaranta ba, inda ya ce su, za su ci gaba da zuwa aiki na tsawon kawa biyar a mako.

Gwamnan Sanwo-Olu ya ce gwamnati za ta yi duk abin da ya kamata domin ƙara wa malaman makarantar tallafin sufuri.

Ciyar da mutum 1000 a kowace rana

Gwamnan ya kuma bayyana aniyar gwamnatin ta ciyar da mutanen da ke rayuwa a jihar aƙalla 1000 a kowace rana.

Ya ce “Za mu zabi masu sayar da abinci (Mama Put) domin samun damar ciyar da aƙalla mutum 1000 a kowace rana a ƙananan hukumomi 20 na jihar tsawon kwana 30 zuwa 60.”

Samar da kasuwannin sayar da abinci cikin rahusa

Gwamnan ya ce gwamnatin Legas za ta samar da kasuwannin sayar da abinci waɗanda ake yi wa laƙabi da ‘Sunday Markets.’

A cewar sa: “Za mu buɗe kasuwanni Lahadi a manyan kasuwanni 42 da aka zaɓo a faɗin jihar.

A irin waɗannan kasuwa za ku iya sayen abinci cikin farashi mai rangwame.”

Ya ƙara da cewa “za a iya sayen kayan abinci waɗanda ba su zarce na naira 25,000 ba ne kawai.”

Haihuwa kyauta

Gwaman ya ce a yanzu kuma gwamnati za ta ɗauki nauyin mata masu haihuwa a asibitocin jihar.

Ya ce za a gudanar da hakan ne a asibitocin gwamnati.

Haihuwa kyautar za ta haɗa har da waɗanda za a yi wa tiyata a lokacin haihuwa.

Haka nan gwamnati za ta yi rangwame a kan farashin wasu magunguna a asibitocin gwamnatin jihar.

Rage farashin sufuri

Sanwo-Olu ya kuma sanar da yin ragowa kan farashin sufuri na kashi 25%.

Rangwamen, wanda zai fara aiki a ƙarshen makon nan zai shafi masu sufuri ne ta motocin safa da jiragen ƙasa da na ruwa na gwamnati.

Haka nan gwamnan ya ce gwamnati na tattaunawa da ƙungiyoyin sufuri domin shawo kansu su rage nasu farashin.

Gwanman dai ya ce gwamnati na sane da halin ƙunci da da al’umma ke ciki kuma ba ta manta da su.

No comments