Daga Zubairu M Lawal Lafia Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya kaddamar da aikin gina hanyar Wamba-Waiye-Dengi-A...
Daga Zubairu M Lawal Lafia
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya kaddamar da aikin gina hanyar Wamba-Waiye-Dengi-Alizaga mai tsawon kilomita 24.5 a Kananan Hukumomin Wamba da Akwanga.
An ba da kwangilar aikin ne ga kamfanin Centerfield Engineering Limited a kan kudi naira biliyan 9,061,627,000.00, kuma ana sa ran hanyar za ta kasance wata muhimmiyar hanya tabunkasa tattalin arzikin jihar. wadda za ta haÉ—a al’ummomi tare da bunkasa harkokin noma, kasuwanci da sauÆ™aÆ™a zirga-zirga.
A cikin jawabin sa, Gwamna Sule ya jaddada muhimmancin gina titunan karkara, yana mai cewa hakan na baiwa manoma damar jigilar kayan amfanin gona da sauran kayayyakin kasuwanci daga kauyuka zuwa birane. Ya kara da cewa gina tutuna a karkara yana da mahimmaci fiye da wasu tituna a birane. Saboda gina titi a karkara hakan mai da karkara ta zama maraya, al'umma suna zurga zurgan gudanar da harkokin kasuwanci dake kawo saukin abinci.
Gwamnan ya bukaci kamfanin da ke aikin da ya bi ka’idoji da tsarin tsaro, tare da roÆ™on al’ummomin da abin ya shafa da su ba da haÉ—in kai ga masu aikin da kuma kare rayuka da kayan aiki.
“Wannan aiki wani É“angare ne na kudirin Gwamnatin Jihar wajen samar da ci gaban ababen more rayuwa domin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da ganin cigaba ya kai kowane yanki,” in ji Gwamna.
Da yake kaddamar da aikin, Gwamna Sule ya sake jaddada kudirin Gwamnatinsa na kada a bar ko wata al’umma a baya wajen kawo ci gaba, domin samar da jihar Nasarawa da tabbatar da lafiya da haÉ—in kan yan jihar.
No comments