Daga Zubairu Lawal Da yake jawabin Shugaban Ƙungiyar yan Dako ta Jihar Nasarawa Alhaji Danji Muhammad Aliyu yayi godiya ga T...
Daga Zubairu Lawal
Da yake jawabin Shugaban Ƙungiyar yan Dako ta Jihar Nasarawa Alhaji Danji Muhammad Aliyu yayi godiya ga Tsofin Shugabanni da membobin kungiyar da mukarrabansa da suke gudanar da mulki tare, bisa goyon bayan da suke bashi na kara wa'adin shekara uku kyauta duk da cewa yana karshen mulki zango na biyu.
Yace; zai daura daga yadda ya tsaya. Kuma kamar yadda yake kawo abubuwan cigaba da kyautawa membobin kungiyar da tsawatarwa da hukunta mai Lefi.
Yace; abaya anyi Shugabanni da suka mulki wannan kungiyar babu Wanda aka taba kara masa wa'adin mulki sai daga kansa.
Yace; wannan kawai ya nuna sun ajiye tarihin na adalci a kungiyar.
Shima Tsohon Shugaban Kungiyar yan Dakon buhu na jihar Nasarawa Alhaji Lawal Yusuf yace; wannan kuddurin Karin wa'adin shekara uku bai sabawa dokar tsarin mulkin kungiyar ba, saboda ba zabe akayi ba, kuma ganin damar ya'yan Ƙungiyar ne.
Yace; sama da mutum 200 suka sanya hannu a takarda suna bukatar a karawa Shugaban da yake kai wa'adi duk da cewa yayi zango biyu.
Yace;; "mun aminche da wannan kuddurin ne saboda yadda Shugaban ke gudanar da mulki bisa adalci da kyautatawa.
mulkin Alhaji Danji Muhammad Aliyu an samu cigaba ta hanyar daukar matasa sama da dari aiki a kungiyar. kuma yawancin membobin kungiyar sun samu damar gina gidajen kwana saboda ba a tauyewa kowa haki.
Sannan a mulkinsa ya samu hadin kai da kamfanoni. Ya kuma baiwa mukarrabansa gurbin gudanar da ayyukan kungiyar bai rike shi kadai ba".
Alhaji Lawal Yusuf ya kara da cewa "muma tsofafin Shugabanni da tsofin kungiya yana kulawa damu".
Yace; a lokacin mulkin Alhaji Danji Muhammad Aliyu an gina katafaren Ofis mallakin kungiyar.
Shima Sakataren kungiyar Ibrahim Lawal Madugu ya jinjinawa Shugaban kungiyar Alhaji Danji Muhammad Aliyu saboda jajircewarsa na kamanta Gaskiya da rikon amana.
Ya yabawa Shugaban kungiyar ta yadda yake baiwa kowa hakinsa na aikin kungiya.
Ya kuma ce; wannan karin wa'adin shekara uku da Membobin kungiyar suka kara masu wato ( Bonos) ya nuna membobin kungiyar sunji dadin Shugabancin Alhaji Danji Muhammad Aliyu da mukarrabansa ke nan.
Yace; samun Shugaba na gari yakansa mukarrabai su zama na gari.
Sakataren yace; duk da cewa wannan tsarin karin wa'adin shekara uku baya cikin kundin tsarin mulkinsu, Amma bai sabawa doka ba, saboda al'umma sune ake mulki kuma sune suka amince da mu cigaba sun karamana wa'adin shekara uku.
Yace; a kungiyar ba rikici akeyiba. Babu tashin hankali. Al'umman kungiyar sama da 200 suka sanya hannu a kan sun aminche da wa'adin.
Kungiyar yan Dakon buhu ta Jihar Nasarawa ta amince da karawa Shugabanta wa'adin shekara Uku kan karagar mulki.
A ranar Lahadi Membobin kungiyar tare da tsofafin Shugabanninta suka gudanar da taro a ofishin kungiyar dake Suto na Kwandare a garin Lafia cikin jihar Nasarawa.
Taron membobin kungiyar ya aminche da kuddurin cigaban da Shugabancin Alhaji Danji Muhammad Aliyu Wanda yake kai tare da mukarrabansa.
Karin wa'adin shekara ukun zai farane nan da watanni biyar, da ya rage masu cikin shekarun mulkinsu.
No comments