Jam'iyyar ADC ta musanta zargin da ta ce ana yaɗawa cewa tana aiki ne domin mayar da mulkin ƙasar zuwa arewacin Najeriya. Kakakin jam...
Jam'iyyar ADC ta musanta zargin da ta ce ana yaɗawa cewa tana aiki ne domin mayar da mulkin ƙasar zuwa arewacin Najeriya.
Kakakin jam'iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi ne ya bayyana haka a zantawarsa da tashar Channels, inda ya bayyana maganar da shashi-faɗi mara tushe.
"ADC jam'iyya ce ta kowa da kowa. Mun faɗa tun da farko cewa ba jam'iyya ba ce ta arewa ko ta kudu. Ba jam'iyya ba ce ta musulmi ko kirista, ba jam'iyya ba ce ta yara ko tsofaffi, jam'iyya ce da aka tsara domin gina Najeriya da tabbatar da muradun ƴaƴanta."
Wannan na zuwa ne bayan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar jam'iyyar a zaɓen baya, Dumebi Kachikwu ya zargi jam'iyyar da yunƙurin tabbatar da ɗan arewa a matsayin shugaban ƙasa.
Abdullahi ya kuma zargi jam'iyya mai mulki da yunƙurin jefa saɓani a jam'iyyar ADC, inda ya ce suna sane, kuma ba su bari ta samu nasara.
No comments