Daga Hussaini Yero Ɗaya daga cikin jigon dan Siyasa a jam'iyyar APC a jihar Zamfara, Sani Abdullahi Wanban Shinkafi ya yi ...
Daga Hussaini Yero
Ɗaya daga cikin jigon dan Siyasa a jam'iyyar APC a jihar Zamfara, Sani Abdullahi Wanban Shinkafi ya yi zargin cewa 'yan siyasa masu yuma gwamnatin jihar Zamfara, Karkashin Jagorancin gwamna Dauda Lawal,Zagon Kasa na shirin cimma burinsu na siyasa, da kira Gwamnatin tarayya ta kafa dokar ta-baci a Zamfara.
Wanban Shinkafi ya bayyana haka ne a zantawa da manema labarai a Gusau, babban Birnin Jihar Zamfara.
A cewar sa, kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya a bayyane yake, wanda ya rufe ido kawai ba zai iya fahimtar me ake nufi ba".
"Bari in fadi a fili cewa Zamfara bata cancanci a ayyana dokar ta baci kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada ba, ya kamata masu daukar nauyinsu su je su karanta da kyau su fahimci abin da tsarin mulki ya ce."inji Shinkafi.
"Ya bayyana cewa sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima yana magana ne kan ayyana dokar ta baci.Musamman ma, ta zayyana sharuddan da shugaban zai iya ayyana dokar ta baci da kuma hanyoyin da ya kamata a bi.
"A dauki misali da Borno inda aka kashe dubbai, wasu kuma suka yi gudun hijira daga Benue, Taraba, Niger da sauran jihohin da ake fama da rashin tsaro,bamu taba jin Wani ya fito daga wadannan jahohin ba sai a Zamfara? ".
Wanban Shinkafi ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa ne ke son kawo tabarbarewar zaman lafiya a Zamfara, shi ya sa suka dauki nauyin ‘yan gudun hijirar domin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da rashin tsaro a jihar, wanda Gwamna Dauda Lawal ya gada daga gwamnatin da ta gabata a jihar.
"Kira da kafa dokar ta-baci a Zamfara aiki ne na 'yan siyasa da ke gudun hijira daga jihar, suna son su durkusar da jihar ne don neman cimma burinsu na siyasa".Ya faɗa.
Ya kuma yi zargin cewa akwai makiya a ciki, wadanda ke taimaka wa ayyukan ‘yan bindiga, wanda ya shawarci hukumomin tsaro a jihar da su haskaka idanunsu, su kuma yi taka tsantsan kan masu zanga-zangar.
Jigon na APC ya kara da cewa,makiyan Zamfarawa ne ke ta kokarin sun tarwarsa cigaban da ake samu a jihar Karkashin Jagorancin gwamna Dauda Lawal da Shugaban Kasa Bula Ahmad Tunubu.
Dan haka Jama'a suyi hattara da wadannan "Yan barandan Siyasa wadanda fatansu shine tarwatsa jihar Zamfara ba cigaban taba.
No comments