A wani taro mai cike da alhini da juyayi da aka gudanar a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, 2025 a muhallin Jannatu Darur Rahma dake Dembo a Z...
A wani taro mai cike da alhini da juyayi da aka gudanar a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, 2025 a muhallin Jannatu Darur Rahma dake Dembo a Zariya, Harkar Musulunci a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky ta gudanar da taron tunawa da cika shekaru 11 da kisan gillar da aka yi wa membobinta 34 a Zariya a yayin wani zanga-zangar lumana ta ranar Qudus a shekarar 2014.
Taron ya kasance cike da jimami da alhini tare da karramawa ga waɗanda suka rasa rayukansu, kazalika an sake jaddada kiran neman adalci. Sannan, Harkar Musuluncin ta bayyana goyon bayanta na dindindin ga al’ummar Falasɗinu da ake zalunta, tana mai cewa kudurinta na tsaya musu tsayin daka bai sauya ba kuma ba zai taɓa gushewa ba.
A yayin ganawarsa da manema labarai a yayin taron, Sayyid Badamasi Yaqoub, dan uwa ga jagoran Harkar Musulunci, ya jaddada cewa; wannan gwagwarmaya da suke yi na neman adalci, dama ta gaji kalubale daga mahukumta; “Dama ita wannan hanya, ita ke nan ba ta da canji. Hanya ce ta kira zuwa ga addinin Allah; to tabbas akwai mutuwa a cikinsa.
Ya ci gaba da cewa; “wannan abin da Annabawa suka sha gwagwarmaya a kai ke nan. Saboda haka da zarar ka ce Allah da ma’anarsa, to za ka hadu da fushin wadanda ba su yarda da wannan ba. Suna ganin su mulkinsu kake kalubalanta, saboda haka lallai ba za su barka ba”, in ji shi.
Sai dai ya ce wadanda aka kashe ba su yi laifin komai ba, illa kawai; “sun ce Ubangijinsu Allah ne, ba su yarda da zalunci ba, suka tsaya a kai”.
Dangane da matakin da za su dauka kuwa, ya tabbatar da cewa su dai za su ci gaba da gwagwarmayarsu, kuma da wannan gwagwarmayar ne karshen zalunci zai zo, kamar yadda ya ce; “Da wannan gwagwarmayar ne karshen zalunci zai zo. Ta wannan yunkuri da suke yi na kisa, ta wannan hanyar ne karshen su zai zo”.
Ya jaddada cewa suna alfahari da wadanda aka kashe, kuma ba za su taba mantawa da su ba. Inda ya jaddada aniyar cewa, wannan ba zai sanyaya musu guiwa ba, za su ci gaba da kasancewa da al’ummar Falasdinu; “Wadannan yara an shahadantar da su ne akan Kudus. Yanzu al’ummar Musulmi su dubi abin da yake faruwa a Gaza. Yanzu mutum ba zai iya kallon abin da yake faruwa a Gaza ba, duk magoya bayansu a kewaye da su, duk kasashen musulmi ne. Ita kanta Isra’ila an kafa ta a kasar Musulmi ne, Masar Musulmi ne, amma kuma sun kewaye sun hana a shiga da abinci, Jordan Musulmi ne, sun kewaye sun hana abinci; kullun ana mutuwa da yunwa, ba abinci ba ruwa, ba komai. Suna bin goyon bayan wadannan azzaluman mahukumta”.
Ya kara da cewa; “Wannan zaluncin da ake yi wa ‘yan’uwanmu a Gaza, muna nan tare da su, kuma wallahi summa tallahi, da za mu samu dama, za mu je Gaza mu bayar da jininmu a kan su”, ya jaddada.
Malam Ibrahim Abubakar, daya daga cikin masu shirya wanna taron, ya tabbatar da cewa suna tuna wannan kisan gilla a duk ranar 25 ga watan Yulin kowacce shekara; “a wannan rana ta 2014 sojojin Nijeriya sun kashe mutum 34, sun raunata akalla mutum 80; masu karami da manyan raunuka. Duk a irin wannan rana idan ta zagayo duk shekara muna haduwa a wannan muhallin na su mu yi musu addu’o’i da saukar Alkur’ani. Sannan mu yi taruka da jawabai na tuna su”.
Ya ce duk wanda ya tsayawa gaskiya zai fuskaci irin wannan. Ya ce a duk inda kake dole a ci gaba da neman hakkin al’ummar Falasdinu.
Tunda farko an soma taron da addu’o’i da karatun Alkur’ani mai girma, tare da gabatar da fareti da kuma jawabai daga Malamai.
Maryam Dalhatu, daya ce daga cikin ‘yan’uwan wadanda aka kashe a wannan rana, ta ce; ta yi farin ciki cewa ana tunawa da su a kowanne shekara, sai dai har yanzu tana kukan rashin su.
Sai dai ta ce; “Sakona ga azzalumai shi ne, wannan hanyar da suka dauka ta kashe mutane, hanya ce ba mai bullewa ba, su sani cewa wannan abin da suke yi ba zai kai su ga ko’ina ba sai asara, tun daga duniya har lahira”, in ji ta.
Kazalika, Alkasim Muhammad Gyallesu, daya daga cikin wadanda aka raunata a wannan rana, shekaru 11 da suka gabata, amma har yanzu illar harbin da aka yi masa na ci gaba da nunawa.
“Ina cikin wadanda sojoji suka harba a lokacin. Ba mu dauke da komai a hannunmu a lokacin, illa iyaka kawai mun fito domin jajen mu da nuna goyon baya tare da Allah-wadai da zaluncin da ake yi ma al’ummar Falasdinu.
No comments