Daga Awwal Umar Kontagora Babban Sakatare na Ƙasa na Ƙungiyar Manoma da Masana'antu da Yan Kasuwa na (ALL GREEN AGRO FIELD...
Daga Awwal Umar Kontagora
Babban Sakatare na Ƙasa na Ƙungiyar Manoma da Masana'antu da Yan Kasuwa na (ALL GREEN AGRO FIELD FARMERS, PROCESSORS AND MARKETERS ASSOCIATION) ta ƙasa, Ambassada (Dr) Nura Hashimu (Tallafin Bosso Karami), ya taya Alhaji Muhammad Babangida, Daraktan Gudanarwa na El-Amin International Schools kuma Shugaban Ƙungiyoyin Polo na Minna da Kaduna, murna bisa naɗin da aka yi masa a matsayin Shugaban Bankin Noma (Bank of Agriculture) da aka sake fasalta ta, daga Maigirma shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
A cikin wata sanarwa da ya sanya hannu da kan sa kuma aka rabawa manema labarai a garin Minna, Amb. (Dr) Nura Hashimu (Tallafin Bosso Karami) ya bayyana nadin Muhammad Babangida wanda shi ne ɗan tsohon Shugaban Soja na ƙasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida a matsayin abin alfahari da kuma cigaba mai kyau ga harkar noma a Najeriya.
Yayin da Tallafin Bosso Karami ke nuna godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa ga zaben da ya yi na Alhaji Muhammadu Babangida, ya kuma bayyana goyon bayan ƙungiyar AGAFAMA ta manoma daga jihohi 36 na ƙasar nan a cikin sabuwar rawar da zai taka.
Amb (Dr) Nura Hashimu, ya bayyana tabbacin cewa nadin da aka yi wa Alh. Muhammad Babangida a matsayin shugaban Bankin Noma zai taka muhimmiyar rawa wajen farfaɗo da harkar noma a jihar Neja da ƙasar baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa, dukkan mambobin ƙungiyar ALL GREEN FARMERS suna alfahari da wannan matsayi da aka ba Alhaji Muhammad Babangida, tare da yi masa fatan nasara da cikakken aiki mai albarka a sabuwar matsayin.
No comments