Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar Matasan Fulani Masu Goyon Bayan Gwamna Bago Za Ta Horar Da Fulani Makiyaya Kan Muhimmancin Rajistan Inshora

Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar 'Fulani Youth Sai Bago Again Organisation' za ta horar da Fulani makiyaya muhimmancin...

Daga Awwal Umar Kontagora

Kungiyar 'Fulani Youth Sai Bago Again Organisation' za ta horar da Fulani makiyaya muhimmancin rajistan Ishora. 

Da yake karin haske ga manema labarai, shugaban kungiyar, Amb. Mujahid Adam yace ganin irin iftila'in da ke aukawa Fulani makiyaya kuma a karshe ba wani tallafin jin kai da suke samu yasa kungiyarsa tunanin janyo masana kiwon lafiyar dabbobi da jami'an hukumomin Inshora dan wayar da yan uwansa muhimmancin yin rajistan Inshora ta yadda idan wani Iftila'in ya aukawa makiyayi zai samu wata damar farfadowa ko rage radadin hasarar da yayi na dukiyarsa.

Ya cigaba da cewar akwai Iftila'o'i da dama da ke samun makiyaya na cututtukan dabbobi da kan zama silar ajalinsu, ko aukowar yan bindiga masu yin awon gaba da dukiyoyin makiyaya, ta yadda idan wani abu ya faru da makiyayi na hasara zai samu damar samun hanyar rage radadi ta hanyar samun Inshora.

Amb. Mujahid, ya cigaba da cewar wannan shirin karawa juna sani da fadakarwa ta rana daya ce a kyauta kuma zai shafi dukkanin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar Neja.

Ya ce, maigirma gwamna, Farmer Umaru Bago ya zo da kudurin taimakawa makiyaya, mu ka dacewar mu goya masa baya, ta hanyar hada taro - sisi daga aljihun mu dan taimakawa gwamnati wajen cigaba da a za harsashen cikar muradun gwamnati ga makiyaya.

Ba mu nemi wani abu daga gwamnati ba, kuma ba mu nemi wata hukuma ta taimaka mana ba. Aikin mun dauko shi ne bil-hakki kuma muna da shiraruwa da dama da za mu gabatar dan cigaban makiyaya da iyalansu kafin cikar wa'adin gwamnatin nan ta yadda koda gwamnatin nan ta kammala wa'adinta za ta iya barin tarihin da makiyaya za su yi alfahari da ita.

Dan haka, ina jawo hankalin matasan mu, musamman wadanda ke karkara da su rungumi neman ilimi da muhimmanci, saboda rashin ilimin nan ne ya jefa da daman matasa ayyukan da ba su dace ba. Ba yadda za a yi mutum mai ilimi ya bari ya tsinci kan shi ga ayyukan da ba su dace ba.

Gwamnatin jiha karkashin ma'aikatar kula da jin dadin makiyaya da manoma ta kaddamar da shirin tattara bayanan makiyaya da dabbobin su, wanda muna sa ran bada jimawa ba, saboda yunkurin samar da abubuwan more rayuwa dole a fara biyan jangali saboda samun kudaden shiga wanda muna goyon bayan shi.

To wani hanya makiyayi zai bi shi ma ya anfana bayan abubuwan more rayuwa, kamar samar da asibitoci da gyara wadanda muke da su, da kuma makarantun Nomadic da muke yunkurin ganin an gyara tare da inganta su. Sannan idan wani Iftila'in ya auku ya za mu samu tallafin kai tsaye dole sai ta hanyar Inshora.

Saboda haka akwai bukatar mu mayar da hankalin mu sosai wajen tabbatar da mun yi rajistan inshorar nan daga kan dukiyoyin mu har iyalan mu, a cewar shugaban.

Sannan iyaye su kara himma wajen kulawa da amanar da Allah ya ba su na kulawa da tarbiyar yayansu, musamman wajen ba su ilimin addini da na zamani, kulawa da harkokinsu na yau da kullun, sannan su tsare dokokin kasa, su guji daukar fansa ko daukar doka a hannun su. Domin daukar doka a hannu shi ke kara karfafa ayyukan yan charge and bel, Wanda a karshe kuma su ke cutuwa.

Shugaban ya bayyana cewar gwamnatin nan ta Farmer Umaru Bago, gwamnati ce da ya kamata a karfafata ta hanyar goya ma ta baya, ya kamata kamar yadda muka fito kwan mu da kwarkwata muka zabi gwamna Umaru Bago, idan hukumar zabe ta fitar da jadawalin yan katin zabe mu umurci yaran mu da suka taso kuma ba su da katin zabe dan mallakar katin saboda cigaba da zubawa gwamna Umaru Bago kuri'un mu duk lokacin da zabe ya taso.

No comments