Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Fara Taron Jin Ra’ayin Jama’a Kan Sauya Kundin Tsarin Mulki A Arewa Maso Yamma A Kano

An fara zaman sauraron ra’ayoyin jama’a na kwanaki biyu a Kano, domin sake duba Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, da nufin ...

An fara zaman sauraron ra’ayoyin jama’a na kwanaki biyu a Kano, domin sake duba Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, da nufin daidaita shi da bukatun zamani. Wannan taro na yankin Arewa maso Yamma da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sauya Kundin Tsarin Mulki ya shirya yana gudana ne a dakin taro na Bristol Palace Hotel da ke cikin birnin Kano.

Taron ya samu halartar wakilai daga jihohi bakwai na yankin: Kano, Jigawa, Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara, ciki har da kungiyoyin fararen hula, masu ruwa da tsaki, sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin ƙwararru, waɗanda ke tattaunawa kan shawarwarin da suka gabatar domin sauya wasu muhimman sassa na kundin tsarin mulki.

A jawabin sa na bude taron, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma Shugaban Kwamitin Sauya Kundin Tsarin Mulki na Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bayyana cewa Majalisar Dattawa ba ta da wani ra’ayi na son rai game da sauye-sauyen, zata saurari ra’ayoyin jama’a domin cimma matsaya ta kasa bisa doka da tsarin majalisa.

Sanata Barau ya jaddada cewa akwai muhimman batutuwa da suka shafi gyaran harkokin zabe, sauya tsarin shari’a, inganta kananan hukumomi, rawar da masarautu za su taka a mulki, kare hakkin bil’adama, da kuma bada dama ga kowa da kowa cikin tsarin mulki. Ya ce an riga an fassara ra’ayoyin jama’a zuwa kudurori domin sake bitar su a wannan taron.

A ƙarshe, Sanata Barau ya yi kira da a hada kai tsakanin Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai, majalisun dokokin jihohi da kuma bangaren zartaswa da na shari’a domin tabbatar da nasarar wannan aikin. Ya ce hadin gwiwa da fahimtar juna tsakanin bangarorin gwamnati na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sauye-sauyen da za su amfani ‘yan Najeriya.

No comments