Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za a Kammala Aikin Gidaje Na Renewed Hope City A Kano Cikin Mako Shida Masu Zuwa — Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta ta kammala aikin gina gidaje na Renewed Hope City da ke Kano cikin mako shida, domin samar...

Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta ta kammala aikin gina gidaje na Renewed Hope City da ke Kano cikin mako shida, domin samar wa ‘yan Najeriya mafita kan matsalar rashin gidaje. Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Ahmad Musa-Dangiwa, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin ziyarar duban aikin da ya kai. 

Ministan ya ce yana gamsuwa da yadda aikin ke tafiya da kuma ingancin aikin da ake yi, yana mai jaddada cewa aikin na tafiya daidai da yadda aka tsara. Ya bayyana cewa mafi yawan aikin da ya rage yanzu ya ta’allaka ne da gyare-gyaren cikin gida da kuma ayyukan wajen gini kamar shigar lantarki da tsarin rarraba ruwa.

Ministan ya samu rakiyar Ƙaramin Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Yusuf Abdullahi Ata, da wasu manyan jami’an ma’aikatar. Aikin na Renewed Hope City yana daga cikin shirin gwamnatin tarayya na rage gibin gidaje a kasar da samar da mafaka mai sauƙi ga ‘yan kasa.

No comments