Daga Awwal Umar Kontagora Kimanin shekara daya ke nan da rikicin Barkuta na karamar hukumar Bosso, rikicin da ya auku tsakanin m...
Daga Awwal Umar Kontagora
Kimanin shekara daya ke nan da rikicin Barkuta na karamar hukumar Bosso, rikicin da ya auku tsakanin manoma da makiyaya da ya lakume rayuka da dukiyoyin jama'a ta dalilin kona gidajen jama'a da rikicin ya auka da su.
Bincike dai ya tabbatar irin wannan rikicin shi ne karo na uku tun daga gwamnatin Dr. Mu'azu Babangida Aliyu har zuwa kan gwamnatin Abubakar Sani Bello ya gangaro kan gwamnatin Dr. Umaru Mohammed Bago. Dukkanin bangarorin biyu tsoffin zama ne a yankin, wanda har zuwa lokacin zamantakewarsu wuri daya bai ba su damar amincewa da juna ba.
Duk irin yunkurin da gwamnatin Neja ke yi bisa jagorancin Dr. Umaru Bago na janyo dukkanin kabilu a jihar, da dama ba su fahimci salon gwamnatin na tafiya da kowa ba, musamman dan a samu zaman lafiya da cigaban mulkin dimukuradiyya ba.
Kan haka gwamnatin ta mayar da hankalinta wajen sulhu, tallafi da yunkurin samar da tsarin kyautatawa rayuwar al'ummar jihar, ta yadda kowani bangaren zai iya bada gudunmawa wajen cigaban jihar.
Bayan faruwar rikicin na baya bayan nan, gwamnatin jiha, ta kafa kwamiti karkashin ma'aikatar kula da jin dadin makiyaya, dan kai tallafi ga wadanda aka konawa gidajensu tare da bada tallafi ba diyya ba ga wadanda suka rasa rayukan yan uwansu. Gwamnatin tace tayi hakan ne dan tausayawa ba wai biyan hasarar da aka yi ba, hakan na nufin jawo hankalin bangarorin biyu dan fahimtar juna da yafiya dan cigaba da zaman tare.
Zaman lafiya, shi zai karfafa guiwar gwamnatin wajen fuskantar tsare tsaren da ke gabanta na cigaban kasa, musamman samar da tsarin ilimi mai inganci, kiwon lafiya, inganta sana'ar noma da kiwo ta yadda kowani dan jiha zai yi alfahari da cigaban da jihar ke samu.
Majiyoyi da dama makusanta ga gwamnatin sun bayyana irin dabaibiyar da tarnakin da ta yiwa tattalin arzikin kasar tarnaki na daga dalilin da ya sanya duk kkudurce kudurcen gwamnatin ke tafiyar hawainiya.
Bincike dai ya nuna mutanen Barkuta da rikicin ya shafa sun tabbatar da cewar gwamnatin jiha karkashin ma'aikatar kula da jin dadin makiyaya da manoma sun kai tallafin kayan abinci da ya kunshi masara da shinkafa, da bargunan rufa da sumunti da kwanon rufi ya isa hannun wadanda aka konawa gidaje tare da tallafin naira dubu dari biyu da hamsin ga iyalan da suka rasa rai a matsayin tallafi ba diyya ba.
Haka kuma, gwamnatin jiha ta umurci makiyaya musamman fulani mazauna yankin da su tabbatar sun mayar da yayansu makaranta, wanda sun amsa wannan umurnin na gwamnatin. Amma abinda suka koka akai shi ne maganar farfado da makarantun Nomadic da ke yankin.
Binciken mu ya tabbatar da cewar kudurce kudurcen gwamnatin nan, a wannan shekarar ta 2025, shekara ce da gwamnatin ta tsara na farfado da makarantun faramare na dukkanin sassan kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar har makarantun Nomadic dari biyu da doriya da ke cikin lissafin gwamnatin amma har zuwa watan bakwai na shekarar ba wanda ya samu, wanda binciken ya tabbatar matsalolin tattalin arziki ne da ya hana gwamnatin nunfasawa ya sanya har zuwa yanzu kudurin bai kai ga matakin nasara ba.
Babban abin lura dai, shi ne zaman lafiya. Kamar yadda bangarorin biyu suka aminta su zauna tare to ya zama tilas su shinfida turbar zaman lafiya, kamar yadda suka shinfido a yanzu, sannan su tabbatar da cewar sun kai zuciya nesa duk abinda ya taso na rashin fahimta su daina daukar doka a hannu, cudanya, mu'amala da zuciya daya zai taimaka masu wajen samun nasara ta hanyar zaman lafiya da cigaban yankin su.
Tsare tsaren gwamnatin Dr. Umaru Bago ga tattalin arzikin jiha, tsari ne da zai kawo cigaban jihar ta hanyar bullo da hanyoyin samun kudaden shiga, samar da sabuwar jihar Neja, da kuma yunkurin gwamnatin na farfado da noma da kiwo da samar da tsarin ilimi ga kowa da kowa, amma hakan ba zai samu ba tilas sai an zauna lafiya tsakanin jinsuna, kabilun jihar don kowa na da rawar takawa da kuma gudunmawar da zai bayar wajen tabbatar da cewar da gaske yake.
No comments