Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Rantsar Da Shugabannin NUMW Na Karamar Hukumar Magama

Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar leboburori masu hakar ma'adanan kasa ta kasa reshen jihar Neja ta rantsar da shugabancin ...

Daga Awwal Umar Kontagora

Kungiyar leboburori masu hakar ma'adanan kasa ta kasa reshen jihar Neja ta rantsar da shugabancin kungiyar na karamar hukumar Magama. Tunda farko a bayaninsa shugaban kungiyar kwadago ta jihar Neja, Comr. Abdukkarim Lafene da ya samu wakilcin shugaban NLC na karamar hukumar Magama, Comr. Umar Adamu Auna ya bayyana cewar wannan kungiyar ba kungiyar siyasa ba ce kungiya ce da ke da hadin guiwa da kungiyar kwadago.

Dan haka, ya jawo hankalin rantsantsun shugabannin da su yi aiki daidai da dokokin kungiyar kwadago ta kasa, da dokokin Nijeriya akan aikin ma'adani wajen kulawa da hakkokin yayan kungiya da tabbatar da adalci ga mambobinta.

"Ku sani ba wata kungiya da za ta hana ku aiki, musamman ganin ku ne dokokin kasar nan ta amincewa yin wannan aikin, dan haka ku dokokin kasa sau da kafa, kuma NLC a shirye take wajen daukar mataki ga duk wani da yayi kutse a cikin ayyukan ku.

Dole ku lalubo hanyoyin samun kudin shiga wanda uwar kungiya ta jiha da ta kasa zasu anfana da wannan muhimmin aikin da aka dora ma ku, dan haka a shirye mu ke a kowani lokaci duk wanda zai yiwa dokar kasa kutse mu dauki matakin da ya dace a kan shi".

A na shi jawabin, kwamishinan ma'aikatar kula da ma'adanan kasa ta jiha, Hon. Garba Sale Auna da ya samu wakilcin daraktan ayyuka na ma'aikatar, Injiniya Isyaku Wando ya baiwa sabbin shugabannin kwarin guiwa, inda yace idan suka bi dokokin gwamnatin tarayya da wanda gwamnatin jiha ta samar zasu gudanar da ayyukan su ba tare da damuwa ba.

Kwamishinan ya janyo hankalin yayan kungiyar da su yi biyayya ga sabbin shugabannin wajen gudanar fa ayyukan su kamar yadda dokokin kungiyar ta tsara wanda gwamnati ta amince da shi, wajen kulawa da kyautatawa mambobinsu, tsayuwa akan hakkinsu da tabbatar da ana gudanar da aiki ba tare da sabawa dokokin kasa ba.

Kwamared Musa Adamu Nasko, shi ne shugaban kungiyar ta jiha, ya yabawa kungiyar kwadago ta jiha bisa goyon bayan da take ba su. A cewarsa nasarorin da kungiyar take samu yanzu ya biyo bayan kyakkyawat fahimtar da ke tsakanin kungiyar kwadagon jiha da gwamnatin jiha, bisa turbar tsaftace harkar hakar ma'adani a jihar Neja.

Kamar yadda muka rantsar da zababbun shugabannin karamar hukumar Magama, haka muke kudurin rantsar da sauran kananan hukumomi idan sun kammala bin tsare tsaren kungiyar mu. Za mu sanya idanu sosai dan ganin ba a kaucewa yarjejeniyar da ke tsakanin mu da gwamnatin jiha ba.

Comr. Bashir Usman shi ne, sabon shugaban kungiyar a karamar hukumar Magama, ya nemi dukkanin leburorin da ke son cin anfanin wannan sana'ar da su tabbatar sun yi rajista da kungiyar su wajen tantancewa da tabbatar da sun mallaki katin shaidar zama da kungiya.

Comr. Bashir, ya bada tabbacin zai yi aiki ba sani, ba sabo dan ganin ba a sabawa dokokin kasa da ta jihar Neja ba, musamman tankade da rairaya dan fitar da baragurbi da na kawarai a harkar hakar ma'adani.

Hajiya Maryam Ibrahim, shugabar mata ta karamar hukumar Magama, ta bayyana cewar mata a shirye suke dan yin gwagwarmayar tankade da rairaya, dan haka za ta cigaba da wayar da kan mata da ke cikin aikin hakar ma'adani, dan ganin ba a bar su baya ba wajen cigaban da aka samu.

Mun dade a wannan harkar kuma mu mata mun san anfanin shi dan ya taimaka mana wajen tsayawa da kafar mu wajen samun madogarar rayuwa da muke talkafawa yayan mu da mazajen mu.

Malam Musa Tela Anfani, daya ne daga cikin iyayen kunvgiyar da aka yi gwagwarmaya da su wajen samar da wannan shugabancin, yace ina da kwarin guiwa, wadannan matasan da aka rantsar yau matasa ne masu amana da su ka dadi da wahalar da ke cikin aikin hakar ma'adani, dan haka mu a matsayin iyaye za mu sanya idanu sosai tare da bada shawarwari dan cigabar harkar hakar ma'adani a wannan karamar hukumar ta mu. 

Barista Mahmud Muhammad, lauyan kungiyar ne ya jagoranci rantsar da mutane goma sha tara cikinsu har da mace daya a garin Anfani da ke karamar hukumar Magama a matsayin shugabannin kungiyar a karamar hukumar Magama.

An dai gudanar da rantsuwar ranar Asabar 26 ga watan Julin 2025. Dukkanin shugabannin kungiyar ta jiha sun halarci rantsuwar.

No comments