Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar matasan Fulani ta Sai Bago Again ta shawarci gwamnatin Neja kan samar da kasuwan dabbobi na z...
Daga Awwal Umar Kontagora
Kungiyar matasan Fulani ta Sai Bago Again ta shawarci gwamnatin Neja kan samar da kasuwan dabbobi na zamani a dukkanin shiyuka uku na jihar.
Bayanin na kunshe ne a wata takardar manema labarai da kungiyar ta fitar yammacin Alhamis din makon nan wanda ya samu sanya hannun shugaban kungiyar, Amb. Dr. Mujahid Adam da sakataren kungiyar Comr. Sulaiman Ruga.
Takardar ta cigaba da cewar samar da kasuwan dabbobi na zamani a shiyukan Neja, ta tsakiya, kudu da arewa zai taimaka wajen samar da gurabun ayyuka ga matasa, samun karin hanyar kudin shiga ga gwamnatin jiha, da dakile barazanar bazuwar dabbobin sata ta hanyar samun saukin cafke duk wata dabbar da aka sato da nufin kai ta kasuwa dan batarwa.
Takardar ta cigaba da cewar irin wannan kasuwar zamani da ake bukata sakamakon kudurin gwamnatin jiha na samar da sabuwar jihar Neja, za a samar da ofishoshin yan sanda da sauran rundunonin tsaro, masaukan baki, da wuraren ibadah da kuma wurin ajiyar motocin dakon kaya, wanda hakan zai bada damar ko bayan kudaden harajin dabbobi, suma motocin dakon kaya zasu rika bada haraji.
Da yake tsokaci akan takatdar, wani matashi kuma mai rajin cigaban gwamnatin jiha, Alhaji Shehu Jita Kango, ya bayyana cewar duba da halin matsalar tattalin arziki da ya hanawa gwamnatin numfasawa wajen gudanar da ayyukan da take bukata, idan gwamnatin Neja ta karbi shawarar koda a shirin hada da yan kasuwa na ( Pupil Private Partnership) za a iya gudanar da ayyukan a dan kankanin lokaci.
Alhaji Shehu Jita, ya cigaba da cewar wannan shawara ce mai kyau, kuma zai taimaka wajen samar da gurabun ayyuka tun daga kan tsaro, haraji da kuma baiwa matasa damar samun gurin gudanar da harkokin rayuwarsu na yau da kullun ba tare da fuskantar wani barazana ba, sannan ita kan ta gwamnatin za ta samu karin hanyar kudaden shiga ta yadda.za ta samu kwarin guiwar gudanar da ayyukan cigaban kasa.
No comments