Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gidauniyyar El-amin Tare Da Haɗin Guiwar Jami'ar El-amin Sun Bada Gudunmawa Ga Cibiyar Tsaro Ta Minna

Daga Awwal Umar Kontagora A ranar 29 ga watan Janairu na shekarar 2025, ɗaliban Jami'ar El-amin, sashen nazarin shari'a ...

Daga Awwal Umar Kontagora

A ranar 29 ga watan Janairu na shekarar 2025, ɗaliban Jami'ar El-amin, sashen nazarin shari'a sun kai ziyara zuwa Cibiyar Tsaro Matsakaiciya da ke Tunga ta Minna a jihar Neja, inda suka yi nazari kan yanayin tsaftar da 'yan fursuna ke ciki, musamman mata.

Bayan ziyarar, rahoton sakamakon ya isa ga shugaban zartarwa (PC), Dr. Muhammad Babangida, wanda ya miƙa shi zuwa Kodineton gidauniyyar El-amin tare da shawarar a bawa ɗaliban damar nuna soyayya da kyautatawa ga marasa galihu/mabuƙata ta hanyar da za su iya. 

Shugaban Jami'ar ya ce hakan ya dace da tsarin shekara-shekara na El-amin Foundation, wanda ke haɗawa da bayar da tallafi ga gidajen yari da kuma shiga cikin shari’o’i da biyan tara domin 'yantar da wasu daga cikin fursunonin da suka cancanta. Duk da cewa jerin sunayen waɗanda za a taimaka musu yana kan bincike, don gudun kar a jinkirta ƙoƙarin ɗaliban Jami'an da ƙara masu ƙaimi, sai  Shugaban Zartarwar Jami'ar ya bayar da izini don a ci-gaba da shirin.

Ɗaliban sun tara gudummawa, El-amin Foundation kuma ta cike sauran gurbi, wanda hakan ya kai ga gabatar da kayayyakin tsafta da aka kai Cibiyar Tsaro Matsakaiciya, Tunga, Minna a ranar Laraba, 6 ga Agusta, 2025.

Kayayyakin da aka bayar sun haɗa da:

1. Buroshin wanke haƙori – guda 300
2. Man wanke haƙori – guda 300
3. Vaseline/Petroleum jelly – guda 300
4. Pad ɗin mata – guda 200
5. Maganin kashe kwayoyin cuta (1 Lita) – guda 100
6. Gidan sauro – guda 100
7. Sabulun wankin kaya – guda 300

Waɗanda suka miƙa kayan sun haɗa da Farfesa Muhammad Bello Uthman (Shugaban Sashen Nazarin Shari’a, EL-AMIN University), Ameera Abbas Bello (Ma’aikaciyar Jami’ar EL-AMIN), da Mr. Bwada Isah Sa'idu (Kwadinato 2, EL-AMIN FOUNDATION - Coordinator 2). AbdulRahman Shagari ya karɓi kayan hannu biyu-biyu a madadin Comptroller, tare da nuna gamsuwa da godiya matuka.

No comments