Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar 'The Huffazul Qur'an And Scholars Association of Nigeria' ta gudanar da karatun A...
Daga Awwal Umar Kontagora
Kungiyar 'The Huffazul Qur'an And Scholars Association of Nigeria' ta gudanar da karatun Al'qur'ani mai tsalki da addu'o'in musamman na zaman lafiya ga kasa karo na takwas.
Tunda farko mai masaukin baki kuma shugaban kungiyar a jihar Neja, Gwani Sheikh Hussaini Abubakar Shakwata ya bayyana cewar tunda farko ya gaji wannan shirin ne ga shugabannin da suka gabata, Gwani Musa Adamu da ya assasa da Gwani marigayi Abubakar Maiturare da ya jaddada kuma aikin bai tsaya domin wannan addu'o'in suna gabatar da shi ne kowace shekara.
Shugaban, ya cigaba da cewar samuwar wannan kungiyar ya samar da nasarori da dama, ta hanyar hada kan malaman tsagaya da samar masu da tagomashi wanda yanzu haka duk abinda za a yi a gwamnatance, gwamnatin na tuntubarsu ta hannun hukumar kula da harkokin addinai ta jiha wanda kungiyar na da wakilci a wannan hukumar.
Ba za mu gushe ba, kamar yadda kowa ya sani babu wata matsalar da za ta taso kuma a mayar da lamarin ba a samu nasara ba. Hakan ne yasa daga cikin ayyukan da kungiyar nan ta sunatar shi ne shirya irin wannan taron duk shekara dan yiwa kasar mu da jihar mu ta Neja da shugabanni addu'o'in musamman saboda samun kwarin guiwa da yiwa kasa da jihar mu ayyukan da suka sanya a gaba.
A na shi jawabin, shugaban Markazul Huffazul Qur'an ta kasa, Gwani Sanusi Abubakar wanda kuma shi ne tsohon sakataren kungiyar ta kasa. Yace bayan kammala wa'adin tsohon shugaban an zabe ni matsayin sabon shugaban kungiyar a wani babban zaben da ya gudana a jihar Bauchi, na assasa tafiyar da hidindimun kungiyar kamar yadda aka saba.
Yau, wannan taron da jihar Neja ke shiryawa shi ne takwas kuma na halarci taruka na biyar ke nan a jihar Neja, bayan nan a jihar Kano mun yi irin wannan taron da mu ka yiwa lakabi da "Yaumul Qur'an" alfanu irin wannan shi ne yiwa kasa addu'o'in musamman, duba da irin halin rashin tsaro, matsalolin yau da kullun da ya shafi shugabanni da al'umma, wanda shi addu'a Ibadah ne, duk lokacin da matsaloli suka taso aka fuskanci Allah da Ikhlasi za a samu mafita.
Gwani Sanusi, ya hori malaman tsangaya da suka cigaba da yiwa kasa addu'o'in zaman lafiya, da kuma horar da almajirai kan riko da Al-qur'ani mai tsalki.
Malam Abubakar Usman Gidado, shi ne mataimakin darakta hukumar Hisba mai kula da Neja ta tsakiya, yace babban abinda ake bukatar bawa da shi, duk abinda zai yi yayi shi da Ikhlasi, karata Al-qur'ani mai tsalki a roki Allah kan bukata abu ne ingantacce saboda hukumarsu za ta cigaba da bada goyon baya ga dukkan ayyukan da ba su sabawa karantarwar addini ba.
Sheikh Umar Faruk Abdallah, shugaban hukumar kula da harkokin addinai ta jiha, da ya samu wakilcin mashawarci na musamman ga hukumar, Malam Abdurrazak Usman, ya yabawa kungiyar Huffazul Qur'an ne bisa cigaba da irin wadannan ayyukan alheri, domin addu'a takobin mumini ne, duk wanda yayi riko da addu'a lallai zai samu mafita ga matsalolin da ke damunsa.
Yace a madadin gwamnatin jiha, hukumar harkokin addinai ta jiha tana na'am da yabawa kungiyar Huffazul Qur'an bisa wannan namijin kokarin irinsa na takwas a jihar Neja.
Hon. Aminu Bobi, shugaban jam'iyyar APC a jihar Neja da ya samu waklicin Alhaji Isma'ila Sidi, ya jawo hankalin malaman tsangaya da su cigaba da kokarin da suke yi na yiwa kasa addu'o'in musamman, dan samun cigaba da bunkasar zaman lafiya.
"Mu shaida ne kan irin gudunmawar da malaman tsangaya ke bayarwa, domin a kowace rana safiya da maraice aka tashi daga makarantun tsangayu ana gudanar da irin wadannan addu'o'in, saboda ba abinda za mu ce face yabawa da karawa malaman mu na addini kwarin guiwa".
Taron addu'o'in dai ya samu halartar kungiyoyin addinin musulunci da ya kunshi yan Tijjaniya, da bangarorin kungiyar JIBWIS na Jos da Kaduna, da Yan Shi'a da Sharifai.
An gudanar da taron addu'o'in ne a babban masallacin juma'ar minna ta jihar Neja ranar Asabar takwas ga watan Agustan nan.
No comments