Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mun shirya horar da makiyaya da manoma muhimmancin zaman lafiya - Kungiyoyin Fulani

Daga Awwal Umar Kontagora Ƙungiyar 'Fulani Youth Initiative of Nigeria' da hadin guiwar 'Fulani Youth Sai Bago Again...

Daga Awwal Umar Kontagora

Ƙungiyar 'Fulani Youth Initiative of Nigeria' da hadin guiwar 'Fulani Youth Sai Bago Again Organisation' ta sha alwashin cigaba da wayar da kan makiyaya da manoma muhimmancin zaman lafiya. Shugaban kungiyar Amb. Dr. Muhammad Mujahid Adam ne ya sha alwashin lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a shirin Zarar Bunu.

Amb. Mujahid ya cigaba da cewar babban kalubalen da ake fuska shi ne barin yara masu tasowa cikin jahilci, wanda tuni kungiyarsa ta fara daukar matakai akan matsalar ilimi ta hanyar samarwa yaran makiyaya da manoma tallafin karatu, wanda yanzu a kallan kungiyarsu da hadin guiwar Ar-Rahmaniyya Foundation sun samarwa yara sama da hamsin tallafin karatu.

Yace ba mu tsaya nan ba, muna da kudurin nan ba da jimawa ba, za mu shirya taron horar da makiyaya da manoma muhimmancin yin rajistan Inshora, ta yadda manoma da makiyaya za su samu saukin yawaitar hasarar dukiyoyinsu ta hanyar fari ko ambaliyar ruwan sama ko wata annobar da ke aukawa dabbobi.

Manufar shirin, shi ne manoma da makiyaya su fahimci irin kudurce kudurcen gwamnatin Neja na kokarin samar da sabuwar jihar Neja, ta yadda kowani dan jiha zai ba da gudunmawa wajen cigaban tattalin arzikin jihar, na samar da kudaden shiga ga gwamnati da kuma morewa ayyukan gwamnatin na cigaban kasa.

Saboda ina jawo hankalin gwamnatin jiha, na fifita ayyukan raya kasa, da bunkasa ilimi musamman ga yayan karkara da karfafa guiwar yayan jiha wajen dogaro da kai ta hanyar riko da sana'o'in hannu sabannin yadda aka raja'a akan ayyukan gwamnati.
Yau, bangaren kiwon lafiya muna baya sosai, idan aka karfafa guiwar matasa akan neman ilimi nan gaba kadan za mu iya samun malaman kiwon lafiya da zasu iya rike kananan asibitocin karkara sabanin wadanda ake baiwa ayyukan kula da makarantun da asibitocin da ke yankunan karkara kuma su kasa sauke nauyin da ke kan su.

Shugaban ya yabawa, babban manoma kuma gwamnan Neja, Dakta Umar Mohammed Bago na kirkiro ma'aikatar kula da jin dadin makiyaya da manoma, hakan ya taimaka gaya wajen samun saukin fuskantar matsalolin da suka dade suna ciwa gwamnatin tuwo a kwarya.

Saboda haka, muna jawo hankalin al'ummomin mu da su baiwa wannan ma'aikatar da gwamnatin jiha goyon baya, dan samun nasarar da ake bukata.

No comments