Rahotanni daga Mali na cewa gwamntin ƙasar ta kama gomman sojoji da take zargi da yunƙurin juyin mulki domin kifar da gwamnatin sojin ƙasar....
Rahotanni daga Mali na cewa gwamntin ƙasar ta kama gomman sojoji da take zargi da yunƙurin juyin mulki domin kifar da gwamnatin sojin ƙasar.
An ce daga cikin sojojin da aka kama har da manyan janarorin sojin ƙasar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunanin takun-saƙa na faɗaɗa a tsakanin sojojin ƙasar wadda ke fama da matsalolin tsaro.
"An kama aƙalla mutum 20 da ake zargi suna da hannu a juyin mulkin," kamar yadda wata majiya ta shaida wa AFP.
Majiyar ta ƙara da cewa daga cikin waɗanda aka kama, "akwai Janar Abass Dembele." Sannan ɗanmajalisar ƙasar ya ce dukka waɗanda aka kama sojoji ne.
Gwamnatin sojin ƙasar, a ƙarƙashin Janar Asimi Goita ta ƙwace mulki ne bayan hamɓarar da gwamnatin ƙasar a shekarar 2020 da 2021.
Kamar yadda AFP ta ruwaito ta hanyar samun bayanai daga wasu majiyoyi daga cikin sojojin ƙasar da ɓangaren gwamnati, sojojin na yunƙurin kifar da gwamnatin ne kafin aka samu nasarar daƙile su.
Kamar Nijar da Burkina Faso, ita ma Mali dai wadda ke da alaƙa da Rasha tana cigaba da fuskantar matsalolin tsaro daga mahara a wasu sassan ƙasar.
No comments