Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

2027: Atiku ya jinkirta karɓar katin ADC saboda rade-raɗin takarar Jonathan

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya jinkirta karɓar katin zama ɗan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) b...

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya jinkirta karɓar katin zama ɗan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) bayan an shirya bikin a Jada, jihar Adamawa, saboda jita-jitar dawowar tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, takarar shugabanci a 2027.

PUNCH ta rawaito cewa ADC na tattaunawa da Jonathan kan tsayawa takara, yayin da wasu magoya bayan Atiku ke matsa masa lamba ya fice daga jam’iyyar idan rikicin ya ci gaba. 

Wani jigo na ADC ya yi ikirarin cewa motsin siyasar Peter Obi ya mamaye sassan kudancin jam’iyyar, lamarin da ke barazana ga burin Atiku kamar yadda jaridar The Punch ta rawaito.

Mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya ce Atiku ba ya jin tsoron kowanne ɗan takara, kuma tsarin rajistarsa a ADC yana tafiya yadda aka tsara. Sai dai wasu jiga-jigan jam’iyyar sun zargi gwamnatin Bola Tinubu da ƙoƙarin tarwatsa shirin Atiku a ADC don rage masa ƙarfi a 2027.

A wani labari, sakataren ƙasa na ADC, Rauf Aregbesola, ya bayyana a Osogbo cewa Allah na tare da jam’iyyar wajen lashe zaben gwamnan Osun a 2026.

No comments