Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Manufar Kafa Ƙungiyar 'Fulani Youth Development Initiative'

Daga Awwal Umar Kontagora Jama'a da dama na makauniyar kallo musamman ganin kafa ƙungiyar 'Fulani Youth Development Init...

Daga Awwal Umar Kontagora

Jama'a da dama na makauniyar kallo musamman ganin kafa ƙungiyar 'Fulani Youth Development Initiative' wadda ta samo asali daga ƙungiyar Fulani Youth Sai Bago Again, bayan kafa ƙungiyar Bago Ruga Ruga wadda tai namijin ƙoƙari a lokacin yaƙin neman zaɓen da ya gabata.

Tunda farko dai ƙungiyar Bago Ruga Ruga da ta assasa shigar al'ummar Fulani siyasa ka'in da na'in bisa turbar ganin gwamnati ta janyo al'ummar Fulani kusa dan cigaba da tafiyar mulkin siyasa tare da su, ya karfafa guiwar gwamnan Neja, babban manomi Umaru Mohammed Bago kirkiro ma'aikatar kula da walwala da jin dadin makiyaya da manoma kuma aka baiwa cikakken Bafillatani damar jan ragamar ma'aikatar.

Hakan yayi tasiri gaya wajen ganin gwamnati ta fara fahimtar ainihin inda ta bukatar samun cikakken ilimi da fahimtar matsalolin da ke damun al'ummar Fulani da Manoma. Wanda gwamna Umaru Bago ya sake jaddada kudurinsa na sauraro da yin sulhu tsakanin Makiyayan da Manoma tunda dukkaninsu akwai kyakkyawar alaka da fahimtar juna tun asali, wannan alakar ne wasu gurbatattu su ka yi yunkurin kifarwa dan cin ma wani bayayyen manufarsu.

Fulani Youth, ta fuskanci irin alheran da gwamnatin Umaru Bago ta zo da shi, da kudurinta na ilmantar da su babban aikin da ke gaban su na samar da kyakkyawar gobe ga matasa masu tasowa yasa ta jajirce wajen shimfida kyawawan manufofi da tsare tsare, ta hanyar bada shawarwari, da kuma lalubo hanyar jinkai dan dogaro da kai.

A yanzu, ta fara yunkuri akan bangaren ilimi, kiwon lafiya, da kuma samar da hanyar karuwar gwamnati wajen samun kudin shiga, tsaro, da jaddada tsarin zamantakewa mai inganci tsakanin manoma da makiyaya ta hanyar yunkurin horar da su da ba su ilimi akan muhimmancin Inshora.

Jagoran tafiyar, cikakken masanin addini kuma kwararren dan boko, wanda ya assasa cibiyoyin ilmin addini da kuma na bangaren kiwon lafiya, bayan gidauniyar tallafin ilimi da sama da matasa dari ke cin anfanin su a yanzu.

Fulani Youth, dai kungiya ce da ke goyon bayan muradun gwamnati na inganta rayuwar al'umma, cigaban kasa da samar da sabuwar jihar Neja. Ta yi shuhura wajen shiga lungu da sako na yankunan karkaru dan sauraren korafe korafen al'umma dan isar da sakon su ga gwamnati.

Bayan kafuwar sabuwar ma'aikatar kula da jin dadin makiyaya da manoma, hakan yayi tasiri gaya wajen samar da sulhu da walwale matsaloli da dama ba tare da an fuskanci jami'an tsaro ba. Bayan bincike ya tabbatar da a kallan rugagen makiyaya da dama sun samu tsaftaccen ruwan sha, da kuma yakewar ganin makiyaya da manoma na yankunan karkara sun mayar da yayan su makatanta dan samun ilimi da zai taimaka masu wajen samun saukin tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum.

Amb. Dr. Muhammad Mujahid Adam, shi jagoran tafiyar Fulani Youth kuma ya jaddada cewar manufa da kudurinsu shi ne samun hadin kai tsakanin gwamnati da makiyaya hususan, hakan ya baiwa kungiyarsa damar yunkurowa wajen wayar da kan makiyaya muhimmancin mallakar katin zabe, dan samun nasarar dawowar gwamnati a lokaci zabuka masu zuwa.

Kungiyar dai ta tabbatar da yunkurin ta na hadin guiwa tare da bada tabbacin hada guiwa da hukumar zaben wajen samun nasarar aikin hukumar nan bada jimawa ba dan ganin yan uwansa Fulani sun mallaki katin zaben, tare da yunkurin ganin yankunan da ya kamata su mallaki runfar zabe sun samu.

Kamar yadda bincike ya tabbatar akwai ayyuka da dama da kungiyar take shirin aiwatarwa ba tare da jiran tallafi daga gwamnati ba, da ya shafi kiwon lafiya, samar da ruwan sha mai tsafta, gyaran makarantun Nomadic da suka lalace, ta hanyar hadin guiwa da kungiyoyi masu zaman kan su.

No comments