Shugaba kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa a bana ba zai shirya wani taron zagayowar ranar haihuwarsa ba, kuma ba ya son wani daga cikin...
Shugaba kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa a bana ba zai shirya wani taron zagayowar ranar haihuwarsa ba, kuma ba ya son wani daga cikin abokansa da mukarrabansa da masu fada a ji a fadin kasar su shirya duk wani taron biki a madadinsa ko da sunan sa saboda kalubalen da Nijeriya ke fama da shi a halin yanzu .
Shugaban ya bukaci abokansa da na kusa da shi wadanda za su iya sanya tallace-tallace na fatan alheri a jaridu don bikin zagayowar ranar haihuwarsa da su ba da gudummawar kudin ga kungiyoyin agaji da suke so da sunan sa.
Shugaban kasar zai yi amfani da wannan dama ta ranar haihuwarsa wajen yin tunani tare da sake sadaukar da kansa kan aikin gina kasa mai cike da kwanciyar hankali, zaman lafiya, wadata da kuma dunkulewar Nijeriya baki daya.
No comments