Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƴan Daba Sun Hallaka Jami'in Sa-kai Na Ƙungiyar AOG (Mafarauta) da wani Yaro A Minna

Daga Awwal Umar Kontagora Rikicin ya barke a wurin wani hakan zinare a yammacin juma'ar nan, rikici wanda rahotanni sun shai...



Daga Awwal Umar Kontagora

Rikicin ya barke a wurin wani hakan zinare a yammacin juma'ar nan, rikici wanda rahotanni sun shaida cewar an fara shi ne tun daga misalin karfe biyar da rabi na yamma har zuwa daren juma'ar, hakar ma'adinan wanda ake yi ba bisa ka'ida ba a cikin garin Minna a unguwar Kwarin-Bege, inda aka ce marigayin sun kai dauki don kwantar da tarzoma, sanadiyyar haka ne cikin Yan daban wani ya sara masa adda akai hakan kuma ya zama ajalin sa har lahira. 

Rikicin ya cigaba da ruwa ruwa har izuwa Flamingo, Maitumbi, David Mark Road dama sauran unguwannin dake da makwaftaka da su a yammacin juma'ar.
Wani rahoton da wakilin Tsalle Daya ya tsegunta ma wakilin mu ya tabbatar mana cewar Yan daban sun wawushe shagunan mutane a Maitumbi tare da awon gaba da kayyaki masu dimbi yawa.

Har zuwa lokacin da muke hada wannan ruhoton akwai labarin cewar Yan daban na nan suna cigaba da cin karen su ba babbaka.

Wasu mazauna unguwar kwarin Bega sun daura alhakin abin da ya faru kan Komishinan Ma'adanai Garba Auna wanda duk da irin koken da sukai tayi ya kasa daukar matakin hana hakan zinari a tsakiyar unguwar su.

Duk da cewar gwamnatin jihar Neja tayi barazanar amfani da bindiga ga Yan daban amma sai gashi lamarin ma na yau yafi na kullum muni.

Tun a baya da kungiyar masu hakar ma'anan kasa ta kasa reshen jihar Neja, karkashin jagorancin Kwamred Musa Adamu Nasko ta nesanta kan ta da duk wani aikin hakar ma'adani bisa umurnin gwamnatin jiha na dakatar da hakar ma'adanai a jihar.

Nasko ya kara da cewar Kwarin Bega bai cikin hurumin mu kuma duk wani halastaccen dan ma'adani yana da takardar shaidar zama dan kumgiya, amma wadannan matasan wasu batagari da ke fakewa dan tada rikici su samu damar yiwa jama'a sata, dan haka muna goyon bayan gwamnatin jiha kan kowani irin mataki da ta ke ganin ya dace da ta dauka dan kawo karshen bata gari.

No comments