Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tsakanin Iran da Isra'ila daga karshe wa zai ci ribar yaki?

Nazari Daga Aliyu Dahiru Aliyu Ita Isra'ila ta dogara da Amerika ne wajen faÉ—a da Iran. Ita kuma Amerika ba ta son fada da I...


Nazari Daga Aliyu Dahiru Aliyu

Ita Isra'ila ta dogara da Amerika ne wajen faÉ—a da Iran. Ita kuma Amerika ba ta son fada da Iran saboda ba ta da riba a ciki. Shi yasa tun baya Amerika ke son ganin tashin hankali a Iran ta cikin gida maimakon kai mata hari duk da za ta iya. To amma ana auna riba da asara ne wajen kowane yaki. Don haka ta ki tunkararta da yakin tun tale-tale sai dai a zuga yan kasar ko a saka takunkumi.

Sannan mafi yawan yan Amerika a yanzu ba sa son Amerika ta shiga yakin da ba nata ba. Kuma a yanzu haka yan kasar na ganin tsirarun yahudawa ne ke juya Amerika. To idan ta shiga yakin nan za a ga ashe abin da ake fada din da gaske ne. Daga nan Joe Biden zai fadi zabe a banza. Shi kam dan siyasa ya fi damuwa da nasarar zabensa akan komai. Don haka ba zai shiga yakin nan ba.

Sannan yaki tsakanin Amerika da Iran zai janyo tsadar man fetur a duniya. A zatonka wa zai ci ribar hakan? Russia! Ita ko a gurin Amerika da Russia ta ci ribar yaki gwara an fasa yakin. Domin daga karshe tattalin arzikinta zai bunkasa. Ka ga kenan karfinta ya kara yawa wajen tunkarar Amerikan. Duk duniya kuwa ba abin da Amerika ta tsana irin abin da zai sa Russia ta yi karfi.

Wani babban dalili kuma shi ne, Iran na kewaye da kasashen da ba za su bawa Amerika damar kai mata hari ba. Afghanistan dai ko shigarta ba za su yi ba, Pakistan ba za su ba su guri ba, Turkey ma haka, Iraq kuwa a hannun Iran take; sai dai ko Azerbaijan. Ita ko sai dai Amerika ta shigeta ta ruwa. To ganin kayan yakin Iran na ruwa da ta samu daga Russia, yana nufin dubban sojojin Amerika za su mutu kafin su isa sansanin yaki. Wannan ma Amerika ba ta shirya masa ba a yakin da ba ta da riba.

Daga karshe dai Isra'ila za a bari ta yi yakinta. Ita kam ba ta da kawaye a Gabas ta Tsakiya da yawa. Dama Larabawa ne kawayenta su kuma ko don rikicin Gaza da shi ne ya janyo har aka zo nan ba za su ba ta dama ba. Karshe sai dai ta dinga kai hari sansanonin yakin Iran a wasu kasashen kamar Syria. Wannan kuma ba yau aka fara ba. Ko kuma su kai hari daya ko biyu a Iran mai nisan zango wanda ba zai zamo cikakken yaki ba. 

Wata babbar matsalar kuma ita ce, Iran tana da yara a kusa da Isra'ila wadanda za su shigar mata yakin. Don haka yakin yafi zuwa kusa da Isra'ila fiye da kusa da Iran. Wanda dama ribar yaki shi ne ya zamana ba a gidanka ake ba. Sannan jama'a su sani Iran fa kasa ce ba kungiya ce kamar H***s ba ko raunana kamar Palestine. Kasa ce mai kawaye da karfin soja. 

Daga karshe dai yakin nan ba lallai ya yi zafi ba. Ina tunanin cewa za a yi tun da Isra'ila ce ta fara kuma aka mayar mata to a zo a yi sulhu. Daga cikin sulhun kuma shi ne sai a ce su fita da Gaza. Wanda wannan kuma nasara ce ga Iran.

No comments