Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaban Ƙasa Ne Ke Iya Magance Matsalar Tsaro Ba Gwamnoni Ba- Sanata Yari

Daga Hussaini Yero Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, mai wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya ba...


Daga Hussaini Yero

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, mai wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya bayyana cewa, shugaban ƙasa ne ke iya magance matsalar tsaro ba gwamnoni ba.

Sanata Yari ya bayyana hakan ne a lokacim da ya ke amsar rahotannin Kwamitin Tallafin Abincin Azumi Da Sallah a Mafara.

Yari ya bayyana cewa, gwamnoni na iyaka ƙoƙarin su na ganin sun yi abin da ya kamata domin kare al'umma daga matsalar hare-haren 'yan bindiga, amma abun ya ci turo sabo da ba su ke da ruwa da tsaki ba wajen tafiyar da Jami'an Tsaro sai shugabani ƙasa.

Kuma su gwamnoni na da sirrin ɓoye da su ke samu ga jama'arsa, za shi ne zai ba Jami'an Tsaro umurnin lallai za a samu nasarar kawar da 'yan ta'addan amma baida wannan damar, in ji Sanata Yari. 

"Da a ce Shugaban ƙasar zai ba gwamnoni dabar ganin sa kai tsaye duk lokacin da matsalar ta taso lallai da an daƙile matsalar 'yan Ta'addan a duk inda suke a fadin ƙasarnan.

Da ya koma kan al'umma kuwa Sanata Yari ya tabbatar da cewa, zuƙatanmu sun gurbata da son rai, rashin tausayin juna dan haka muke shan wuya da tsadar rayuwa. Amma idan muka gyara zuƙatanmu mu ka ji tausayin junan mu lallai Allah zai agaje mu daga halin da muke ciki, in ji shi. 

No comments