Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matasa Za Su Huta A Gwamnatin Uba Sani, In Ji Aysha Ahmed

Daga Fatima Idris, Zaria A lokacin da Barista Aysha Ahmad Muhammad, take miƙa saƙon ƙaramar sallar bana a taron Hawan Barikin da...


Daga Fatima Idris, Zaria

A lokacin da Barista Aysha Ahmad Muhammad, take miƙa saƙon ƙaramar sallar bana a taron Hawan Barikin da ya gudana a masarautar Zazzau wanda mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya gudanar don miƙa saƙon godiya ga mai girma Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani a babban filin wasan Polo dake GRA Zariya, Barista Aysha Ahmad ta yi godiya ne ga Allah tare da jinjina ga al'ummar ƙasar Zazzau bisa yadda suka tarbi mataimakiyar Gwamnan Hajiya Dakta Hadiza Balaraba a wannan lokacin da ta zo Zariya don wakiltar mai girma Gwamnan jihar Kaduna a hawan Bariki na wannan sallar, ta ce, Allah ya saka masu da Alkhairi.

Barista Aysha ta yi tsokaci game da ƙudurorin gwamnatin jihar Kaduna a ɓangaren karfafa rayuwar matasa don tabbatar da harkar dogaro da kai a faɗin jihar baki ɗaya, har ta ƙara da cewa matasa za su huta a Gwamnatin Uba Sani da ikon Allah.

Ta ce Gwamnatin Uba Sani za ta ci gaba da antayo kuɗade ta asusun jama'a har sai an kori zaman banza da zaman ƙashe wando a da'irar matasan jihar Kaduna baki ɗaya.

Barista Aysha dai matashiyar mace ce mai kishin ci gaban al'umma mai taimako al'umma gida da waje.

Ta zama mai marawa jam'iyar APC baya tare da kawo hanyar ci gaban jam'iyya a faÉ—in jihar Kaduna baki É—aya.

Don haka ta yi kira ga al'ummar jihar Kaduna da su ci gaba da bai wa Gwamna da mataimakiyarsa baya a kowani lokaci .

Ta yi godiya ga Allah bisa yadda aka fara taron lafiya aka gama lafiya.

No comments