Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sarkin Kagara Ya cika shekaru uku kan karagar mulki

Daga Awwal Umar Kontagora Mai martaba sarkin Kagara, Malam Ahmad Garba Gunna II ya cika shekaru uku kan karagar mulki, a bayanin...


Daga Awwal Umar Kontagora

Mai martaba sarkin Kagara, Malam Ahmad Garba Gunna II ya cika shekaru uku kan karagar mulki, a bayaninsa bayan kammala sallar Idi karama lokacin da yake karban gaisuwa. Mai martaba ya godewa Allah bisa damar da ya samu na gadon wannan kujerar, haka ya roki Allah kan ya gafarta masu kurakuran da suka yi na tsawon shekaru uku kan karagar mulkin sarautar Kagara.

Mallam Ahmad Garba Gunna II, ya nemi al'ummar karamar hukumar Rafi da su ajiye bambance bambancen da ke tsakaninsu, harshe ko addini, ko siyasa wajen hada kai dan ciyar da kasar Kagara gaba.

Mai martaba, yace kofa a bude take duk inda jama'a suka hangi kuskure su sanar da majalisar masarauta tare da bada shawarwarin gyara, domin dan Adam tara yake bai cika goma ba, a kowani lokaci kofarsa a bude take wajen karban gyara da shawarwari. Idan jama'a sun tsaya akan neman kuskure dan samun dama, wannan sun mika al'amarin ga ubangiji, wanda ya ga kuskure ya gyara mai martaba ya neman masa lada wajen Allah subhanahu wata'ala.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, bayan kammala zantawarsa da mai martaba sarki, shugaban karamar hukumar Rafi, Hon. Ayuba Usman Katako, ya godewa Allah bisa jarabawar da Allah ya kawo wa kasar Rafi, yace wannan al'amari jarabawa ne daga Allah kuma mun mika komai gare shi.

Saboda haka, ina jadaddawa al'ummar Rafi bisa jajircewar manomi gwamna Umar Bago, Allah zai ba mu mafita. Yanzu bisa kokarin da gwamnati da jami'an tsaro ke yi, da yardar Allah matsalar tsaro a kasar Rafi zai zama tarihi nan bada jimawa ba. Ina kira ga al'ummar Rafi, da mu hada kai mu gina kasar Rafi, mu kara jajircewa wajen yiwa kasar Rafi addu'a na neman mafita daga wannan halin rashin tsaron.

Burin mu a wannan damar ta bana manoma su koma matsugunnin su dan cigaba da aikin gona kamar yadda kudurin gwamnatin jiha na dawo da martaba noma a jihar nan ya cika. Saboda haka ina kara tabbatarwa al'ummar Rafi gwamnati za ta cigaba da yin tsayin daka sosai tare da hadin kan jami'an  tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Hon. Zubairu Isma'ila ( Zannan Kwangwama, Cigarin Tungan Bako) dan majalisar jiha mai waklitar karamar hukumar Rafi, yace matakan da gwamnati ke dauka kan matsalar tsaro abin a yaba ne, yace yanzu haka gwamnati ta amince da kara yawan jami'an tsaro a yankin Tegina, Kusharki da Pandogari da Kagara wanda hakan ya taimaka gaya wajen saukin hare haren yan ta'adda a yankin.
Dan majalisar yace yanzu haka gwamnati na daukar wasu sabbin matakai na ganin an murkushe matsalar tsaro baki daya a yankin, wanda ba lallai a sanar da kafafen yada labarai irin matakan ba.

Da ya juya kan kudurin gwamnatin jiha na dawo da martabar noma, su a majalisa suna maraba da shi, sai dai dan majalisar ya koka kan aikin madatsar ruwa na Zara, yace ya kamata manomi gwamna Umar Bago, in har yana da kudurin mutanen Rafi su anfani kudurin gwamnatin shi, to ya tabbatar ya karbe aikin daga hannun kamfanin Biwater zuwa kamfanin da suka shirya aiki kuma suke da kayan aiki.
Madatsar ruwa na Zara kadai, idan aka samu nasarar kammala shi daruruwan matasa ne zasu samu aikin yi, kuma za a iya noma ridi da sauran nau'ukan abincin da za a iya fitar da shi waje mai dimbin yawa.

Da ya juya kan sauyin siyasa kuwa, yace bayan zuwan sa majalisa, yazo da dubarun da al'umma zasu ci romon dimukuradiyya, ta hanyar koyar da su sana'o'in ta yadda zasu dogara da kafarsu da kuma dauke hankalin su akan damuwa na hasarurrukan da kasar Rafi tayi sanadiyar rashin tsaro.
Dan majalisar ya nemi al'ummar Rafi da su cigaba da baiwa gwamnati goyon baya, domin kudurin wannan gwamnatin na ciyar da jihar Neja gaba, shi yasa gwamnati ta bullo da sabuwar kudurin samar da sabuwar jihar Neja.

Sheikh Aminu Yahaya Abdullahi Balarabe, shi ya jagoranci sallar idin na bana. A hudubarsa yayi kira ga al'umma da su koma ga Allah, kowa yasan irin rawar da yake takawa wajen sabawa Allah, to jama'a su gaggauta tuba, tuba kuma na gaskiya.

Shehin malamin, yace manoma, masu arziki su ji tsoron Allah, su rika cire hakkin Allah a cikin dukiyarsu, na Zakka, Sadaka da taimakekeniya ga mabuka. Idan mu ka gyara Allah zai lizamci lamurran mu, zai kare watsuwar jinainayin mu da dukiyoyin mu.

A kashen Aminu Balarabe, ya nemi jama'a su kara kaimi wajen yin addu'o'in zaman lafiya da yiwa shugabanni biyayya da taimakon da su da adfu'o'in wajen samun nasarar sauke nauyin da ke wuyarsu.

No comments