Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Leicester City Ta Koma Gasar Firimiya Bayan An Doke Leeds

Leicester City ta samu tikitin komawa gasar Premier bayan Queens Park Rangers ta doke Leeds United. Da kashin da kungiyar ta Daniel Farke 4-...


Leicester City ta samu tikitin komawa gasar Premier bayan Queens Park Rangers ta doke Leeds United.

Da kashin da kungiyar ta Daniel Farke 4-0, yanzu akwai tazarar maki hudu tsakaninta da Leicester City da ke matsayi na daya kuma wasa guda ne ya rage.

Foxes na neman haÉ—a maki 100 a hanyarsu ta komawa gasar Premier bayan fadawa gasar Championship.

Yanzu Leicester za ta iya dukan ƙirji ta ce ta lashe kofin sannan kuma ta yi murnar lashewa a gidan Ipswich da ke matsayi na uku.

Ipswich za ta iya biyo bayan Leicester zuwa Premier idan ta samu maki biyar cikin wasanni uku da suka rage mata.


No comments