Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rigimar Salah Da Klopp: Idan Na Yi Magana Ɓaci Za Ta Yi - Salah

Dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah ya ce idan ya daɗi abin da ya shiga tsakaninsa da kocin ƙungiyar Jurgen Klopp a wasan da ƙungiyar ...



Dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah ya ce idan ya daɗi abin da ya shiga tsakaninsa da kocin ƙungiyar Jurgen Klopp a wasan da ƙungiyar ta tashi kunnen doki da West Ham ''ɓaci abin zai yi''.

An ga Mohamed Salah na musayar yawu da Jurgen Klopp a lokacin da yake shirin shiga fafatawar a minti na 79.

A nasa ɓangaren, Jurgen Klopp ya ce shi ma ba zai faɗi abin ya shiga tsakaninsa da Salah ba.

Sai dai tsohon ɗan wasan ƙungiyar Peter Crouch ya faɗa wa kafar yaɗa labarai ta TNT Sport cewa lamarin ba zai zame wa ƙungiyar ''alkairi ba''.

"Salah ɗan wasa ne da aka fara mafi rinjayen wasannin ƙungiyar da shi, don haka dole ba zai ji daɗi ba idan aka ajiye shi a benchi ," in ji Crouch.

"Amma ba wanda zai so ganin irin wannan tsamin dangantaka tsakanin fitaccen ɗan wasa da kuma koci."

An ga alamar Salah ya ji haushi kan wani abu da Klopp ya faɗa masa a lokacin da yake shirin shiga wasan, kuma da alama ya so ci gaba da mayar da martani kafin abokan wasansa Darwin Nunez da Joe Gomez su haƙurƙurtar da shi.

Sakamakon wasan na nuna cewa Liverpool ta fice daga kokawar ɗaukar kofin Premier na bana.

Ƙungiyar na mataki na uku, kuma a yanzu fatan da kawai ya rage mata, shi ne Arsenal da Manchester City su yi rashin nasara a wasanninsu na gaba.

No comments